Jump to content

Gidado Idris

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gidado Idris
Secretary to the Government of the Federation (en) Fassara

17 Oktoba 1995 - 28 Mayu 1999
Rayuwa
Haihuwa Zariya, 15 ga Maris, 1935
Mutuwa 15 Disamba 2017
Karatu
Makaranta University of Leeds (en) Fassara
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Gidado Idris, GCON (15 ga Maris 1935 - 15 December 2017) ma’aikacin gwamnati ne dan Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnati da Shugaban Ma’aikatan tarayya a Najeriya tsakanin 1993-1999, a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Gidado Idris an haife shi ne a cikin dangin masarautar Sokoto. Asalin sunansa Usman. Giɗaɗo, sunan da daga baya aka san shi, kalma ce ta Fulatanci wacce ke nufin "ƙaunatacce". Yawanci sunan laƙabi ne.

Giɗaɗo an haife shi kuma ya girma a Zariya, inda kakanninsa suka yi ƙaura sakamakon rasuwar mahaifinsu Gidado dan Laima don komawa cikin dangin mahaifiyarsu ta Malam Musa, wanda yake aiki a lokacin yana mai mulkin Zazzau. Daularsu ana ƙiranta da Mallawa a Zariya, jihar Kaduna.

Giɗaɗo yayi karatun sa na farko a Zaria. Ya tafi makarantar firamare ta Zariya daga 1942–46, da kuma Makarantar Midiya ta Zariya daga 1952-1957. Daga baya ya wuce zuwa Cibiyar Gudanarwa, Zariya da Jami'ar Leeds da ke Ingila. Ya shiga aikin gwamnati kafin samun 'yancin kan Najeriya kuma yana cikin wannan aikin har zuwa 1999.

Wasu Ayyuka

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aiki a matsayin Sakatare na musamman ga Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato sannan kuma ya yi aiki a matsayin Hakimin Gundumar (DO) a lokuta daban-daban a Benuwai, Sardauna da Lardunan Adamawa na yankin Arewa na wancan lokacin. Haƙiƙa yana tare da Sardauna sa’o’i kafin wasu sojoji masu kisan gilla su kashe Firimiya a lokacin juyin mulkin soja na farko a ranar 15 ga Janairun 1966. Daga nan wannan ma’aikacin ya yi aiki a matsayin Babban Sakatare a rusasshiyar Jihar Arewa ta Tsakiya, yanzu jihohin Kaduna da Katsina daga 1971-75. An nada shi Sakataren Kwamitin Tsara Tsarin Mulki [CDC] a karkashin Cif Rotimi Williams a 1975 kuma a 1976 ya yi aiki a matsayin Sakataren Majalisar Kundin Tsarin Mulki wanda ya samar da Tsarin Mulki na 1979 wanda ya kawo Jamhuriya ta Biyu. A cikin shekaru hudu na Jamhuriya ta Biyu [1979-83], Alhaji Gidado Idris shi ma ya kasance a matsayin magatakarda ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

https://dailynigerian.com/news/abachas-sgf-gidado-idris-dies-82/ Archived 2017-12-26 at the Wayback Machine

http://leadership.ng/2017/12/18/gidado-idris-technocrat-goes-home/ Archived 2020-10-12 at the Wayback Machine

https://aledeh.com/flash-gidado-idris-former-nigerias-sgf-dies/[permanent dead link]

https://www.vanguardngr.com/2015/03/gidado-idris-80/