Jump to content

Gidan Tarihin Fasaha ta Yankin Ternopil

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Gidan Tarihin Fasaha ta Yankin Ternopil
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaUkraniya
Oblast of Ukraine (en) FassaraTernopil Oblast (en) Fassara
Raion of Ukraine (en) FassaraTernopil Raion (en) Fassara
Amalgamated hromada (en) FassaraTernopil Hromada (en) Fassara
City of regional significance of Ukraine (en) FassaraTernopil (en) Fassara
Coordinates 49°33′26″N 25°35′34″E / 49.55725°N 25.59275°E / 49.55725; 25.59275
Map
History and use
Opening1 Mayu 1991
Contact
Address вул. Соломії Крушельницької, 1а, Тернопіль, Україна

Gidan Kayan Tarihin Fasaha ta Yankin Ternopil gidan kayan gargajiya ne a yankin arewa ta tsakiyar Ternopil, Ukraine. An kafa shi a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1991 a mazaunin tsohon gidan kayan gargajiya - sashen gidan kayan gargajiya na yankin kabilu.[1] Gidan kayan gargajiya yana da kudirin bincike akan haja, ilimi (laccoci da ziyarce-ziyarce), baje koli, nunin faifai, aikin dabaru da sabuntawa.kayayyakin da ke gidan tarihin sun haɗa da zane-zane, sassaka-sassake, fasaha da fikira. Daga cikin abubuwan nune-nunen akwai gumaka na ƙarni na 17 zuwa 19, zane-zane na Johann Georg Pinsel da Anton Osinskyi . Nuni na dindindin ya dogara ne akan tsari na tarihi da na zamani kuma yana wakiltar fasahar Ukraine da Yammacin Turai.

Gidan kayan tarihi na fasaha yana da dogon tarihi. Ya fara ne daga gidan kayan tarihi na yankin Podil'skyi, wanda aka buɗe a ranar 13 ga Afrilun shekarar 1913. Wanda ya kafa gidan tarihin shine Farfesa S. Sorokivskyi. Ya kuma yi aiki da farko a gidan kayan tarihin a matsayin jagora. Daga cikin abubuwan da aka baje kolin har da ayyukan ƙwararrun zane-zane da sassaka, kafet da kayan kwalliya, tsabar kuɗi, takaddun asali. A lokacin yakin duniya na farko, Rashawa sun lalata kayan tarihin.

Ayyuka da nuni

[gyara sashe | gyara masomin]

Kayan dake gidan tarihin ya zuwa 1 ga watan Janairun shekara ta 2009 yana dauke da abubuwa guda 8011 ciki har da zane-zane - 765, zane-zanen fenti - 6965, sassake-sassake- 140, fasaha da fikira guda - 141. Abubuwan gani na dindindin sun dogara ne akan tsari na tarihi da na zamani kuma suna wakiltar fasahar Ukraine da Yammacin Turai.

Daga cikin abubuwan da aka nuna na fasahar mutan en Ukraine akwai gumaka na karni na 17 zuwa 19, zane-zane JG Pinsel da Anton Osinskyi, hotuna, littattafan tarihi tare da zane-zane daga karni na 18.

Dioniziy Sholdra sanannen mai dawo da kayan tarihi kuma mai zane daga New York wanda aka haife shi a Ternopil, ya yi aiki a Gidan kayan tarihi na Art a tsakanin 1993 – 1995. Ya ba gidan kayan gargajiya zane-zane 50 kuma ya aza kafa tushe mai armashi.

A Satumban shekarar 1998 ne aka bude Memorial Hall D. Sholdry, inda aka nuna ayyuka, hotuna da takardu, kayan aikin sabuntawa da kayan aiki, kayayyakin mutane na masu zane.

  1. "karpaty.info. "Art Museum — Ternopil". www.karpaty.info. Retrieved 2021-01-28.