Gideon Obhkhan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gideon Obhkhan
Rayuwa
Sana'a

Gideon Obhkhan ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon kwamishinan ilimi a jihar Edo. Ya tsaya takarar majalisar wakilai a loƙacin babban zaɓen 2015.

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Gideon Obhkhan a Ekpoma, Jihar Edo, Najeriya. Ya halarci makarantar firamare ta Emaudo, Ekpoma, kafin ya wuce zuwa Kwalejin Katolika ta Annunciation, Irrua inda ya yi karatun sakandire daga nan ya wuce Jami'ar Benin inda ya sami digiri na farko a Injiniyan lantarki. Ya yi digirinsa na biyu a fannin injiniyan sadarwa daga Jami'ar Legas kafin ya wuce Jami'ar Leicester, United Kingdom don yin karatun MBA. [1]

Sana'a da siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Obhkhan ya yi aiki da kamfanonin sadarwa masu zaman kansu kamar su Mobitel da EMIS sadarwa kafin ya koma MTN Nigeria a matsayin manajin darakta, Tsare-tsare da Dabaru.

Obhkhan ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a zaɓen 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa, Joe Edionwele na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Gwamnan jihar Edo na lokacin Adams Oshiomhole ne ya naɗa shi kwamishinan ilimi . A lokacin zaɓen gwamna na 2020 a jihar Edo, ɗan takarar jam’iyyar PDP ya nada shi daraktan bincike na ƙungiyar yakin neman zaɓen Ize-Iyamo.

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Obhkhan Kirista ne kuma yana da aure.[ana buƙatar hujja]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0