Ginin Sakatariyar Tarayya
Appearance
Sakatariyar Tarayya bene ne mai hawa 15 a Ikoyi, Legas.[1][2]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An gina benen ne a shekarar 1976 don ma'aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya. Makasudin ginin ya tsaya a 1991 bayan da aka mayar da matsayin Legas a matsayin babban birnin Najeriya zuwa Abuja, FCT.
Tun a shekara ta 2006, ginin ta kasance a cikin takaddamar shari’a tsakanin gwamnatin jihar Legas da wani kamfanin kera kadarori (Resort International Limited) wanda ya samu nasara a shari'ar don cigaba da gudanar da ginin daga hannun gwamnatin tarayya.
Duk da cewa hukumar NAFDAC ta na amfani da wani bangare na ginin na wucin gadi ginin ya kasance a cikin wani wuri da aka watsar da shi a tsawon rayuwarsa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Dayo Ayeyemi (June 14, 2022). "FG Has Lost N88bn Revenue To Abandoned Old Federal Secretariat Ikoyi In 27 Years'". Nigerian Tribune. Retrieved August 28, 2022.
- ↑ "Restore Lagos federal secretariat complex, Society of Engineers urges govt". The Punch. Retrieved August 28, 2022.