Gokana
Gokana Karamar Hukuma ce dake Jihar Rivers a shiyar kudu maso kudancin Nijeriya.
Hedikwatar ƙaramar hukumar na cikin garin Kpor . Yankin ya kunshi garuruwa da dama da suka hada da Yeghe, Gbe, Goi, Bakora, Kibangba , Bomu , Deken , da Bera . Adadin al'ummar ƙaramar hukumar Gokana ya kai mutane 194,713 inda mafi yawancin mazauna yankin yan ƙabilar Ogoni ne . Addinin Kiristanci shine addinin da yafi yawan mabiya a Yankin . Grebe Mene na ƙaramar hukumar Gokana shine mai kula da gargajiya . Muhimman bukukuwan da ake gudanarwa a yankin sun haɗa da bikin Naa Bira Dae. Ƙaramar hukumar Gokana tana kan fadin kasa murabba'in kilomita 126 kuma tana da koguna da magudanan ruwa dake ratsa cikin yankinta . Matsakaicin zafin jiki na karamar hukumar ya kai 26 digiri centigrade yayin da matsakaicin yanayin zafin yankin shine kashi 87. Noma wani muhimmin aiki ne na tattalin arziki a ƙaramar hukumar Gokana inda ake noma amfanin gona da dama kamar plantain, dabino, rogo, okro , da ayaba da duk ana nomawa a yankin . Sauran muhimman sana'o'in tattalin arzikin al'ummar ƙaramar hukumar Gokana sun hada da kasuwanci, ginin gidaje, kamun kifi , da gina kwale - kwale.