Jump to content

Gokana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Gokana, Jihar Rivers)
Mai magana da yaran igbo
Gan garin gokana

Gokana Karamar Hukuma ce dake Jihar Rivers a shiyar kudu maso kudancin Nijeriya.

Hedikwatar ƙaramar hukumar na cikin garin Kpor. Yankin ya kunshi garuruwa da dama da suka hada da Yeghe, Gbe, Goi, Bakora, Kibangba , Bomu , Deken , da Bera . Adadin al'ummar ƙaramar hukumar Gokana ya kai mutane 194,713 inda mafi yawancin mazauna yankin yan ƙabilar Ogoni ne. Addinin Kiristanci shine addinin da yafi yawan mabiya a Yankin. Grebe Mene na ƙaramar hukumar Gokana shine mai kula da gargajiya. Muhimman bukukuwan da ake gudanarwa a yankin sun haɗa da bikin Naa Bira Dae. Ƙaramar hukumar Gokana tana kan fadin kasa murabba'in kilomita 126 kuma tana da koguna da magudanan ruwa dake ratsa cikin yankinta. Matsakaicin zafin jiki na karamar hukumar ya kai 26 digiri centigrade yayin da matsakaicin yanayin zafin yankin shine kashi 87. Noma wani muhimmin aiki ne na tattalin arziki a ƙaramar hukumar Gokana inda ake noma amfanin gona da dama kamar plantain, dabino, rogo, okro , da ayaba da duk ana nomawa a yankin. Sauran muhimman sana'o'in tattalin arzikin al'ummar ƙaramar hukumar Gokana sun hada da kasuwanci, ginin gidaje, kamun kifi , da gina kwale - kwale.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.