Gong Li
|
| |||
1998 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Shenyang (en) | ||
| ƙasa |
Sin Singapore | ||
| Ƴan uwa | |||
| Abokiyar zama |
Ooi Hoe Seong (en) Jean-Michel Jarre (mul) | ||
| Ma'aurata |
Zhang Yimou (en) | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Central Academy of Drama (en) (1985 - | ||
| Harsuna |
Sinanci Faransanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | jarumi da ɗan wasan kwaikwayo | ||
| Tsayi | 1.6 m | ||
| Muhimman ayyuka |
Red Sorghum (en) Raise the Red Lantern (en) Memoirs of a Geisha (en) Farewell My Concubine (en) The Story of Qiu Ju (en) | ||
| Kyaututtuka |
gani
| ||
| IMDb | nm0000084 | ||
Gong Li ( Sinanci : 巩俐; an haife ta a ranar 31 ga watan Disamba, 1965) 'yar fim ce' ƴar asalin ƙasar Singafo wacce aka haifa a ƙasar Sin, ana ɗaukarta a matsayin ɗaya daga cikin kyawawan mata a China a yau. Ta yi fice a cikin uku daga cikin Kyaututtuka huɗu na Finafinan duniya mafi kayatarwa da aka yi su da yaren China.
Kuruciya
[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Gong Li ne a garin Shenyang, Liaoning, China, ita ce auta a jerin yara biyar din da iyayenta suka haifa. Mahaifinta farfesa ne a fannin tattalin arziƙi kuma mahaifiyar ta malama ce. Ta girma ne a Jinan, babban birnin Shandong . Ta kasance mai son waƙa da rawa tun tana ƙarama, kuma tana da burin zama mawaƙiya.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]1987–1989: Farawar aikinta
[gyara sashe | gyara masomin]
A shekarar 1987, wani darakta mai suna Zhang Yimou ya fara zabar Gong don taka rawa a cikin wani shirin yakin nuna kin jinin Japan mai suna Red Sorghum, wanda a hukumance ya ƙaddamar da haɗin kansu na tsawon shekaru 15 tare da daraktocin ƙarni na biyar na ƙasar Sin. Fim din ya lashe Gwarzon Zinare a bikin Fim na Ƙasa da Ƙasa karo na 38 a Berlin, ya zama fim din kasar Sin na farko da ya fara samun wannan kyauta. Hakanan ya sami lambar yabo ta Golden Rooster da Kyautar Furanni Dari a matsayin fim Mafi Kyawun Hoto a cikin shekara ta 1988.