Grace Kodindo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Grace Kodindo
Rayuwa
Haihuwa Doba (en) Fassara, 19 Disamba 1950 (73 shekaru)
ƙasa Cadi
Karatu
Makaranta Université de Montréal (en) Fassara
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a gynaecologist (en) Fassara
Employers Université de N'Djaména (en) Fassara

Grace Kodindo (an haife ta ne a shekarar 1960) likita ce 'yar ƙasar Chadi da ta karanci fannin kula da lafiyar mata masu juja biyu da kuma karɓar haihuwar yara da ta samu lambar yabo a sashen inganta haihuwa da kiwon lafiya, ba kawai a Chadi ba har da sauran ƙasashen duniya dake fama da talauci. An bayyana ta a cikin shirye-shiryen gidan rediyon BBC guda biyu: Dead Mums Don't Cry (2005), don nuna yadda take ƙoƙari wajen ganin an samu raguwar yawan mace-macen mata masu ciki da kuma masu haihuwa, da kuma Grace Under Fire (2009), da ke bayar da rahoto kan shigar ta cikin shirin kiwon lafiyar haihuwa. a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Kuruciya da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Grace Kodindo a Doba, a kudancin Chadi, a shekarar 1960. Ita 'yar Jean Kodindo Demba ce, wanda ya kasance jami'in gwamnati. Kamar 'yan uwanta maza da mata da suke iyaye ɗaya da sauran 'yan uwanta da suke kofa daban, an saka ta a makaranta. Bayan ta kammala karatunta na makarantar sakandare a Lycée Félix inboué a N'Djamena, ta sami tallafi daga gwamnatin Kanada wanda ya ba ta damar yin karatu a jami'ar Montreal inda ta halarci makarantar koyon aikin likita.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]