Jump to content

Gundumar Anloga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gundumar Anloga


Wuri
Map
 5°48′N 0°54′E / 5.8°N 0.9°E / 5.8; 0.9
Ƴantacciyar ƙasaGhana
Yankuna na GhanaYankin Volta
Labarin ƙasa
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Guinea
Sun raba iyaka da
wani wuri a angola
Gundumar Anloga
Gundumar Anloga

Gundumar Anloga na ɗaya daga cikin gundumomi goma sha takwas 18 a Yankin Volta, Na kasar Ghana. Asali yana daga cikin gundumar Keta mafi girma a lokacin a ranar 10 ga watan Maris shekarar alif dari tara da tamanin da tara 1989, wanda aka ƙirƙira shi daga tsohuwar Majalisar Gundumar Anlo. Ko yaya a ranar 19 ga Fabrairun shekarar 2019, yankin yamma na gundumar ya rabu don ƙirƙirar Gundumar Anloga a matsayin ɗayan gundumomi shida da Gwamnatin Akufo-Addo ta buɗe,[1][2] don haka sauran ɓangaren an riƙe su a matsayin Gundumar Karamar Hukumar Keta. Majalisar gundumar tana cikin kudu maso gabas na Yankin Volta kuma tana da Anloga a matsayin babban birninta.

Wurare masu yawa a Yankin

[gyara sashe | gyara masomin]

Babban gari a cikin gundumar shine babban birnin, Anloga. Wasu daga cikin kauyukan sun hada da Alakple, Kodzi, Dzita, Dewegodo, Dewenu, Srogboe, Whuti, Atito, Fiaxor, Deta, Genui, Benadzi, Azanu, Apklorfudzi, Tregui, Trekume, Bleamezado, Dosukorpe, Lividzi, Agortoe, Salo, Fiato,Kpɔɖui,Adzato, Tegbi, Nyikutor, Suipe, Dzita, Bomigo, Ƒuveme, Anyaŋui, Tunu, Akplowotorkor, and others.[3]

Babban kabila a Gundumar Anloga su ne mutanen Ewe. Babban rukunin Ewe sune Anlo Ewe. Shugabansu kuma sarkinsu shine Awormefia na Anlo, Togbui Sri na III.[1]

Gundumar tana zaune ne a Anloga. Shugaban gwamnatinta shine Hakimin Gundumar (DCE) wanda Shugaban Ghana ya nada. (DCE) na yanzu shine Seth Yormenu.[4]

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. 1.0 1.1 "New Anloga District Inaugurated". voltaregion.gov.gh. Volta Regional Coordinating Council. Retrieved 21 July 2020.
  2. "Government to inaugurate six new districts today". ghanaweb.com. GhanaWeb. 19 February 2019. Archived from the original on 21 July 2020. Retrieved 21 July 2020.
  3. "Agavedzi residents call for support after tidal waves render 700 homeless - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-29.
  4. "Group wants Anlo DCE removed over alleged corruption". myjoyonline.com.gh. 18 September 2019. Retrieved 21 July 2020.