Hafsat Shehu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hafsat Shehu tsohuwar jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood, Kuma mata ga fitaccen jarumi Margayi Ahmad S Nuhu, tana ɗaya daga cikin kyawawan mata a masana'antar kannywood a wancan lokaci, Kuma[1] Hafsat Shehu ta yi tashe a masana'antar fim ta Hausa.[2]Jarumar ta yi fina finai da dama irin su:

Yayi

Tutar So

Sakata

Zabbari

Da sauran su

Takaitaccen Tarihin Ta[gyara sashe | gyara masomin]

An haife a ranar 28 ga watan nuwamba a shekarar 1986 a garin Kano jihar Kano, tayi karatun firamare a Kano daga Nan tai sakandiri a makarantar gwamnatin ta mata ta shekarau ta gama a shekarar 2003, bayan Nan Bata Dora karatu ba ta fada harkan fim , da yarjewar iyayenta babanta da kansa ya damka ta a hannun sarki Ali nuhu, inda tace Ali nuhu ya kula da ita tamkar yar uwarsa ta jini,fim din data fara Yi shine fim din(kamshi)Wanda ya Kuma fitowa da ita shine fim din (zabbari).

A wurin Shirin fim din ta hadu da Ahmad S Nuhu margayi, inda suka fara soyayyah harta Kai su ga aure, auren soyayyah da fahimtan juna, Ahmad ya rasu a hanyar sa ta Maiduguri zuwa wasan sallah hadarin mota,ya rasu ya barta da ciki, bayan mutuwar sa ta Kara yin Wani auren , auren be jima ba ta fito.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.