Jump to content

Haidar Hadi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Haidar Mansour Hadi Al-Athari (an haife shi a ranar 27 ga watan Yulin shekarata alif 1970), wanda akafi sani da Haidar Hadi, ɗan siyasan Iraki ne wanda a halin yanzu yake aiki a matsayin jakadan Jamhuriyar Iraki a Rasha da kuma Belarus . An haife shi a Bagadaza, Iraki ya tafi makaranta a garinsu kuma ya koma Ingila a shekarar alif 1991. Bayan kammala karatunsa daga jami'a a Burtaniya yayi aiki a matsayin manajan fitarwa na Kamfanin Canary Trading Company Limited daga shekarata alif 1997 zuwa shekarar 2000. A shekara ta 2000, ya ɗauki matsayin Manajan Shirin a Webstar PLC har zuwa shekara ta 2003. Daga nan sai ya koma Jordan da farko kafinnan ya koma Iraki. Ya kasance jakadan gwamnatin Iraqi tun watan Oktoba shekarata 2009. Haidar ya riga yayi aiki a matsayin jakada a Minsk, Belarus na shekaru biyar da rabi kuma jakada a Moscow, Rasha na shekaru uku. Shine jakadan Iraqi na farko da yayi aiki a Belarus tun lokacin da aka rufe ofishin jakadancin Iraqi a shekara ta 2003, bayan mamayar Amurka a Iraki. Komawa a Ma'aikatar Harkokin Waje a Bagadaza, Haidar ya jagoranci Ma'aikatu ta Turai har sai an tura shi Rasha a karo na biyu a watan Yunin shekarata 2024.