Hajiya Zainab Maina
Hajiya Zainab Maina | |||
---|---|---|---|
2011 - 2015 ← Josephine Anenih - Aisha Alhassan → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 7 ga Augusta, 1948 (76 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Hajiya Zainab Maina, FCIA, MFR (an haife ta ranar 7 ga watan Agusta, 1948) a Jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya. Ta kasance tsohuwar ministan mata da walwalar jama'a ta Gwamnatin Tarayya Najeriya, wadda aka nada ta a watan Yulin shekarar 2011.[1][2]
Ilimi da Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Zainab Maina ta fito ne daga jihar Adamawa dake Arewa Maso Gabashin Najeriya. Ta yi karatu a "Kaduna Polytechnic" inda ta samu Diploma a fannin Gudanarwa da kuma karatun gaba da Diploma ND a fannin girke-girke da kula a otel (Catering and Hotel Management). Bugu da kari, ta kuma samu shaidar karatun sakataranci (Secretarial Studies) a "Federal Training Centre Kaduna" , sannan kuma a cibiyar "Centre for Development & Population, Washington DC", dake USA inda ta samu karatu a kan "Institution Building Activities" .
Sannan Kuma ta auri Alhaji Umar Joji Maina, dan-Malikin Mubi dake Jihar Adamawa kuma suna da 'ya'ya tare.
Aikin Gwamnati da kuma Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin a ba ta matsayin minista a cikin watan Julin 2011, Maina ta kasance:
- Board Chairman, National Commission for Nomadic Education, Kaduna (2009–2011);
- Board Chairman, Garki Microfinance Bank (1998);
- Board Chairman, NCWS, Garki Microfinance Bank, Abuja (1997);
- Deputy Chairman, Police Community Relations Committee FCT Command (1998-Date);
- Member, Vision 2010 Committee (1997);
- Board Member, National Programme on Immunization (1998–2000);
- Board Member, Adamawa State Primary Schools Board (1991–1994);
- Board Member, Family Economic Advancement Programme (FEAP) (1997–2000).
Ta kasance shugabar kungiyar National Council for Women Societies (NCWS) na Najeriya. Maina na daga cikin masu fada aji a jam'iyyar PDP mai ci na lokacin sannan ta kasance memba na kwamitin dattawa na PDP, majalisar amintattu na jam'iyyar, da darekta ta musamman a fannin harkokin mata a kamfe na tshohon shugaba Jonathan da mataimakin shi Namadi Sambo (2010), Kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyar PDP (2010); Wakiliyar mata ta kasa, Majalisar kamfe na shugaban kasa na jam'iyyar PDP (2007), Wakiliya a taron National Political Reform Conference (NPRC)-2005; Wakiliyar Mata na kwamitin sulhu na jam'iyyar PDP "PDP Reconciliation Committee on theExecutive/Legislative Impasse" (2002); Mai saukan baki na kasa da kasa na taron Home Economics and Consumer Affairs International Council of Women (ICW) da aka yi a Bangkok,Thailand (1993).[2]
Ayyukan da ba na Gwamnati ba
[gyara sashe | gyara masomin]- Founder/President, Women for Peace Initiative (WOPI) Nigeria
- Patron, Young Muslim Women Association, Nigeria
- Sub-Regional Coordinator- Anglophone Africa, International Council for Women
- Member, World Association of NGOs (WANGO)
- Member, West African Civil Society Forum (WACSOF)
- INGO Ambassador, International Non-Governmental Organization(London, UK)
Lambobin Yabo da Karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]- National Award of Excellence towards Women Development Abuja, Nigeria
- Jean Harris Award – Rotary International
- Winner of the Distinguished Eagle Achievement Award Newark, New Jersey, USA
- Amazon Women Award for Contribution towards the Development of Womanhood, Lagos, Nigeria.
- Africa Youth Congress Award on the authority of the Senate Headquarters, Banjul, the Gambia
- Merit Award by the Mayor of Atlanta, USA
- Meritorious Certificate for Loyal and Devoted Services to Development by the Nawar-U-Deen Society of Nigeria
- Certificate of Recognition – University of Kansas, Lawrence, USA
- Quintessence Award for Remarkable Contribution to Humanity by media in support of Humanity (MISH)
- Ambassador for peace by the Universal Peace Federation and the Inter-Religious and International federation for world peace
- Honorary citizen of Kansas City, USA
- Fellow, African Business School – FABS
- Fellow Chartered Institute of Administration – FCIA
- Member of the Order of the Federal Republic – MFR
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Oduah-Ogiemwonyi is new aviation minister, Maina heads women affairs". The Sun (Nigeria). 4 July 2011. Archived from the original on 8 July 2011. Retrieved 18 July 2011.
- ↑ 2.0 2.1 "Hajiya Zainab Maina Biography - Age, Family". MyBioHub. 2018-06-04. Retrieved 2022-03-25.