Halim (fim)
Appearance
| Halim (fim) | |
|---|---|
| Asali | |
| Lokacin bugawa | 2006 |
| Asalin harshe | Larabci |
| Ƙasar asali | Misra |
| Characteristics | |
| Genre (en) |
biographical film (en) |
| Direction and screenplay | |
| Darekta | Sherif Arafa |
| 'yan wasa | |
| Samar | |
| Mai tsarawa |
Emad Adeeb (en) |
| External links | |
Halim ( Larabci: حليم) wani fim ne na ƙasar Masar da aka sake a shekarar 2006 a game da mawakin Masar Abdel Halim Hafez.[1] A shekarar 2005 aka fara shirya fim tare da Ahmed Zaki a matsayin jarumi, amma jarumin ya rasu kafin kammala fim ɗin, don haka dansa (Haitham Ahmed Zaki) ya maye gurbinsa a fage da dama. An saki fim ɗin a cikin watan Yuli 2006 tare da Mona Zaki, Sulaf Fawakherji, wanda Sherif Arafa ya ba da umarni, Mahfouz Abd El-Rahman ya rubuta, Ammar El Sherei ma kiɗi kuma Kamfanin Good News 4 Film & Music Company ne ya shirya. An sanya fim ɗin a gasar Cannes Film Festival na 2006.[2]
'Yan wasa
[gyara sashe | gyara masomin]- Ahmed Zaki a matsayin Abdel Halim Hafez
- Haitham Ahmed Zaki a matsayin Abdel Halim Hafez - Matashi
- Mona Zaki a matsayin Nawal
- Jamal Suliman a matsayin Ramzi
- Sulaf Fawakherji a matsayin Jeehan
- Ezzat Abou Aouf a matsayin Mohammed Abdel Wahab