Halima Kyari Joda
Hon. Hajiya Halima Kyari Joda (Alkaman Gudi), mace ce ta farko da ta dare karagar shugabancin karamar hukuma a fadin jihar Yobe, wato Shugabar karamar hukumar Fika da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.[1] Halima Joda Kyari an haife ta ne a garin Gadaka a Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe, kuma Yar kabilar Ngamo ce da ke Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe. Mutuniyar karkara ce, a can aka haife ta. Baban ta hedimasta (Headmaster) ne wato shugaban malaman firamare.[2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Tayi makarantar Firamare a Central da ke garin Potiskum. Bayan ta gama nan sai ta tafi Kwalejin gwamnati wato G.S.S. Nguru, ta samu shaidar kammala sakandare. Daga nan sai aka yi mata aure. Bayan nan sai ta tafi Kwalejin aikin gona ta samu Difloma a fannin raya gandun daji daga nan sai ta kara ta tafi Jami’ar Maiduguri inda ta samu shaidar digiri na farko a bangaren nazarin harsuna.[3]
Kwasa-kwasai
[gyara sashe | gyara masomin]Hajiya Halima ta je kwas a College of Agro Forestry a Maguga da ke Nairobi a Kenya da Gonar Mai Zube wato Mai Zube Farms da ke garin Minna, a Jihar Neja da kuma School of Forestry dake garin Kano.[4]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Tayi aiki a ma’aikatar kula da gandun daji, da ma’aikatar gona da kuma ma’aikatar tsaftace muhalli a Jihar Yobe amma ta taso da matukar sha’awar aikin kungiya ne, amma ba ta fara aikin kungiya ba sai da ta yi ritaya don kashin kanta a shekarar 2012. da ta yi ritaya sai ta ci gaba da ayyukan kungiyoyi da taimakon kai- da- kai.
Nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]Hajiya ta samu nasarori sosai domin a lokacin da take aikin gwamnati a ma’aikatun kare gandun daji ta kare muhalli da ma’aikatar aikin gona, ta tsaya sosai wajen ganin ba a cutar da wani ba kuma duk inda aka samu matsalar muhalli sukan je su warware matsalar.
Bugugu da kari, ta samu nasarar lashe zaɓen kujerar shugaban karamar hukumar Fika a karkashin jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar ranar 27 ga watan Fabrairu 2021.
Kalubale
[gyara sashe | gyara masomin]Tun lokacin da take aikin gwamnati ta saba da kalubale saboda babban kalubalen shi ne hada aikin gida da na ofis da kuma rainon yara. A bangaren aikin kungiya ma kasancewar ta na shugabancin National Council for Women Society of Nigeria (NCWS) Majalisar kungiyar mata ta kasa tana sanya ido kan yadda ake cin zarafin mata ta hanyar fyade wasu Iyayen suna boye yarsu idan aka mata fyade, wanda hakan bai taimaka wa. Tsayuwar su ne kan haka ya sa har Gwamna Ibrahim Gaidam a lokacin mulkinsa ya bullo da dokar daurin rai da rai kan duk wanda aka kama da laifin fyade.
Kungiyoyi
[gyara sashe | gyara masomin]Kungiyoyin Kasashen da take ciki su ne: National Council for Women Society of Nigeria (NCWS) da Kungiyar Masu Noman Shinkafa da kuma kungiyar dukkan manona ta kasa (All Farmers Association of Nigeria) sai kuma Kungiyar Sun flower Association da Kungiyar Manoman Alkama (Wheat farmers Association).
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://independent.ng/lg-poll-apc-female-candidate-gets-royal-blessings-in-yobe/
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/burina-in-zama-muryar-marasa-murya-hajiya-halima-joda-kyari
- ↑ https://hausa.leadership.ng/bunkasa-rayuwar-alumma-shi-ne-babbar-buri-na-hon-hajiya-kyari-joda/amp/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-05-29. Retrieved 2022-05-29.