Jump to content

Hari a wurin Jana'iza a Kuda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hari a wurin Jana'iza a Kuda
attack (en) Fassara
Bayanai
Kwanan wata 16 ga Yuni, 2016
Perpetrator (en) Fassara Boko Haram
Wuri
Map
 9°20′N 12°30′E / 9.33°N 12.5°E / 9.33; 12.5


A ranar 16 ga watan Yunin 2016 ne ƙungiyar Boko Haram ta kai wani hari a wani wurin jana’iza a Kuda, Najeriya.[1][2]

A yammacin ranar 16 ga watan Yunin 2016 ne wasu gungun ‘yan bindiga daga ƙungiyar Boko Haram masu da’awar jihadi suka isa Kuda, wani ƙauye kusa da Madagali a arewacin jihar Adamawa da ke a arewa maso gabashin Najeriya, bisa babura.[1][2] A lokacin ana jana'izar wani shugaban yankin. [1][2] Ƴan ta’addan sun buɗe wuta kan masu jana'izar inda suka kashe aƙalla 18 daga cikinsu tare da jikkata wasu aƙalla 10.[1][2] Maharan sun kuma yi awon gaba da abinci tare da ƙona gidaje.[1][2]

A baya ƙungiyar Boko Haram sun kai hari a wannan kauyan a watan Fabrairun 2016.[2]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Boko Haram murder 24 at village funeral – mostly women". The Guardian. 2016-06-17. Archived from the original on 2022-12-09.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 "Boko Haram kills 18 women at a funeral in Nigeria". Al Jazeera. Archived from the original on 2023-07-10.