Hasan Mahmud (dan siyasa)


Muhammad Hasan Mahmud (an haife shi a ranar 5 ga Yunin shekarar 1963) ɗan siyasan Bangladesh Awami ne wanda shine ɗan majalisa mai ci daga mazaɓar Chittagong-7.[1] A cikin Janairu 2019, ya naɗa a matsayin Ministan Yaɗa Labarai na Bangladesh.[2] Shi ma babban sakataren haɗin gwiwa ne na ƙungiyar Awami ta Bangladesh.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Muhammad Hasan Mahmud a ranar 5 ga watan Yuni 1963 a Chittagong.Ya kammala digirinsa na farko da na biyu a fannin ilmin sinadarai daga Jami'ar Chittagong a 1987 da 1989 bi da bi.[3]Ya kammala masters na biyu daga Vrije Universiteit Brussel a kimiyyar muhalli a 1996.[4] Ya sami digirinsa na digiri na uku a fannin ilimin kimiyyar muhalli daga Jami'ar Transnational Limburg a 2001.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Acikin 1977, Mahmud ya koma Bangladesh Chhatra League.
Acikin shekarar 1996-2001,Mahmud ya zama mashawarcin firaminista Sheikh Hasina kan harkokin siyasa da majalisa.A shekara ta 2001, an naɗa shi mataimaki na musamman ga shugabar 'yan adawa ta majalisar dokokin ƙasar, Sheikh Hasina. An naɗa shi Sakataren Muhalli da Daji na Awami League.
Mahmud shi ne ɗan Jatiya Sangsad daga mazaɓar Chittagong-6 a tsakanin 2008-2014.[5]Ya samu kuri'u 101,340 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Nationalist ta Bangladesh Salahuddin Quader Chowdhury ya samu kuri'u 72,073.[6]
An naɗa Mahmud a matsayin ƙaramin ministan harkokin waje a watan Janairun 2009 a majalisar ministocin Sheikh Hasina amma bayan watanni 6 ya zama ƙaramin ministan muhalli da gandun daji.[7][8][9] Acikin Nuwamba 2011, an ƙara masa girma zuwa cikakken ministan muhalli da gandun daji kuma ya yi aiki har zuwa ƙarshen 2013.[10][11]

An zaɓi zabi Mahmud ne dan majalisa daga Chittagong-7 a shekarar 2014 a matsayin dan takarar jam'iyyar Awami League a zaɓen da ba a yi takara ba. A zaben dai kashi 50 cikin 100 na kujerun sun samu ne ba tare da jefa kuri'a ba yayin da babbar jam'iyyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party ta jagoranci kawancen kauracewa zaɓen.
An sake zaɓen Mahmud a majalisar wakilai daga Chittagong-7 a shekarar 2018 a matsayin dan takarar jam'iyyar Awami League. Ya samu kuri'u 217,155 yayin da abokin hamayyarsa na Liberal Democratic Party, Md Nurul Alam, ya samu ƙuri'u 6,065.

A watan Satumba na 2022, an zaɓi Mahmud a matsayin hukumar zaben wakilan ƙaramar hukumar Awami League. Sakatare Md Mokbul Hossain a ma’aikatar yada labarai a karkashin Mahmud an tura shi yin ritayar dole a watan Oktoba.[12][13]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Mahmud ya auri Nuran Fatema Hasan.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "List of 10th Parliament Members". Bangladesh Parliament. Archived from the original on 28 September 2018. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "47-member new cabinet announced". The Daily Star. 6 January 2019. Retrieved 8 January 2019.
- ↑ "Profile Of Ministers". The Daily Star. 9 January 2009. Archived from the original on 26 January 2013. Retrieved 28 November 2018.
- ↑ "Bangladesh Sangbad Sangstha (BSS)". BSS. Archived from the original on 2021-06-20. Retrieved 2022-10-18.
- ↑ "List of 9th Parliament Members". Bangladesh Parliament (in Bengali). Archived from the original on 31 July 2023. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "Electoral Area Result Statistics". Amarmp (in Turanci). Archived from the original on 2022-10-18. Retrieved 2022-10-18.
- ↑ "Hasina chooses 25 novice ministers, makes personal physician foreign minister". Thaindian. Indo-Asian News Service. 6 January 2009. Archived from the original on 17 November 2015. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "Hasan Mahmud removed from foreign min". bdnews24.com. 31 July 2009. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "Govt forms 26 parliamentary bodies". BanglaNews24. 2 April 2014. Archived from the original on 17 November 2015. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "Two of the old guard made ministers". The Daily Star. 29 November 2011. Retrieved 29 November 2018.
- ↑ Tusher, Hasan Jahid; Hasan, Rashidul; Bin Habib, Wasim (13 January 2014). "Many go, a few stay". The Daily Star. Retrieved 13 November 2015.
- ↑ "Info secretary Mokbul Hossain sent on retirement". The Business Standard (in Turanci). 2022-10-16. Retrieved 2022-10-18.
- ↑ Report, Star Digital (2022-10-18). "Ex-info secretary Mokbul's "financial scam": HC wants to know ACC action". The Daily Star (in Turanci). Retrieved 2022-10-18.