Hasna Mohamed Dato
Hasna Mohamed Dato | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
2004 - 2009
2003 - 2008
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Obock Region (en) , 10 Nuwamba, 1959 (64 shekaru) | ||||||
ƙasa | Jibuti | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | People's Rally for Progress (en) |
Hasna Mohamed Dato (an haife ta 10 ga watan Nuwamba 1959 [1]) 'yar siyasar kasar Djibouti ce kuma memba ce ta Majalisar Dokokin Pan-Afirka daga Djibouti .
An haifi Dato ne a Obock kuma memba ce ta People's Rally for Progress (RPP). An zabe ta a Majalisar Dokokin Djibouti a Zaben majalisar dokoki na Janairu 2003 [1] a matsayinta na ‘yar takara na 35 a jerin sunayen 'yan takarar Union for a Presidential Majority (UMP) na hadin kai a Yankin Djibouti. Bayan wannan zaben, an zabe ta a matsayin Sakatariya me ba da rahoto akan Hukumar Shari'a da Manyan Gudanarwa a Majalisar Dokoki a ranar 26 ga Janairun 2003.[2]
A ranar 10 ga watan Maris na shekara ta 2004, Majalisar Dokoki ta Kasa ta zabi Dato a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisa biyar na farko na Majalisar Dokokin Afirka.[3][4]
Dubi kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin mambobin majalisar dokokin Pan-Afirka
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Short CV at National Assembly website" (in Faransanci). Archived from the original on December 2, 2005. Retrieved 2016-11-10.. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "CV" defined multiple times with different content - ↑ "Les parlementaires procèdent a l'élections des membres des différentes commissions et bureaux de l’Assemblée Nationale" Archived 2005-01-20 at the Wayback Machine, ADI, 26 January 2003 (in French).
- ↑ "Tenue d'une session extraordinaire de l'Assemblée Nationale" Archived 2005-01-20 at the Wayback Machine, ADI, 10 March 2004 (in French).
- ↑ "Trois projets de lois adoptés en session extraordinaire" Archived 2004-05-30 at the Wayback Machine, La Nation, 11 March 2004 (in French).