Hassan Sarkin Dogarai
Hassan Adamu da akafi sani da Hassan sarkin dogarai shine dogari na uku 3 wanda sarkin kano Ado Bayero ya nada, Ya zama Sarkin dogarawan Sarkin Kano a shekara ta alif 1990. Jama'a sun kara sanin sa dalilin wakar da marigayi Mamman Shata ya yi masa mai taken Hassan Sarkin Dogarai
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Hassan Adamu sarkin dogarai a shekara ta alif dari tara da ashirin da biyar (1925)
Nadin Sarkin Dogarai
[gyara sashe | gyara masomin]Hassan Adamu ya kasance Sarkin Dogarai na Uku Da Marigayi Sarkin kano, Mai Martaba Alh Ado Bayero Ya Naɗa a matsayin Shugaban Dogarawan Sarki a Shekarar alif 1990. Kafin Nadin Hassan a Matsayin Sarkin Dogarawan Fadan Kano, Marigayin yana da Wasu Mutane biyu Daban a baya, akwai dan wudil da Adamu, kuma Bayan mutuwar Adamu ne Aka Nada Hassan,Shima bayan mutuwar Hassan a kanada Dan'bala.
Sana'ar Tukin Mota
[gyara sashe | gyara masomin]Hassan ba Bafade bane, asalin sa direba ne dake Sana'ar tuka mota Kafin daga baya Yazama hadimi ga Galadiman Kani, marigayi Tijjani Hashim, Mutumin daya fara nadashi a matsayin Shamakinsa,Kuma yazama sanadiyyar Shigar sa Cikin fadar Kano.[1]
A shekarar 1990 ne, Bayan mutuwar Sarkin Dogarai dan-wudil, Marigayi galadiman Kano, Tijjani Hashim, yaroki Sarkin Kano Mai martaba Ado Bayero Alfarma yanada Hassan a matsayin Sarkin Dogarai, Saboda tsananin biyayyarsa da kuma jarumtarsa, Sannan ga Soyayya da yake nunawa ga Sarkin. Sarkin dogarai kafin Rasuwarsa yana zaune tare da Iyalansa a unguwar sagagi kusa da Gidan mahaifiyar Sarki Ado Bayero.Kafin daga bisani ya koma Gidan Sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, dake kusada gidan Sarkin Kano. Hassan yayi shura a chikin Sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da Jarumta Da kuma tsananin Biyayyansa ga Sarki Ado.[2] Hassan tsayayyan mutum ne, Saboda girma da tsayi har kirari akeyi masa da bishiya.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hassan ya rasu a shekarar 2007. Yanzu haka Iyalan Hassan sun koma unguwan sagagi asalin gidan mahaifinsu Suncigaba da rayuwarsu bayan Rasuwar sa.