Helen Prest-Ajayi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Helen Prest-Ajayi
Rayuwa
Haihuwa 17 Oktoba 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta King's College London (en) Fassara
Jami'ar Obafemi Awolowo
International School Ibadan (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Lauya da Mai gasan kyau

Helen Perst-Ajayi, tsohuwar Perst-Davies, ( née Perst, an haife ta 17 ga watan Satumba 1959) lauya ce a Nijeriya, marubuciya kuma tsohuwar sarauniyar kyau.[1] Helen ta tashi ne a Ingila . Ta halarci Makarantar International School ta Ibadan domin ci gaban ta da kuma Jami’ar Obafemi Awolowo ta yi karatun digirin farko a fannin Shari’a tun kafin ta fara gasar. Bayan an nada ta sarautar Miss Nigeria tana da shekaru 19 a 1979, ta wakilci Najeriya a gasar sarauniyar kyau ta duniya kuma ta ci gaba da karatunta a King's College London, ta samu LLM. Ta kuma kasance mai aiki a matsayin marubuci a cikin 1990s. A yanzu haka ita ce Shugabar Kamfanin Kasuwanci na Media. Ita jika ce ga ɗan siyasan Najeriya Arthur Perst kuma ɗiyar ɗan siyasa Cif Michael Godwin Perst. Tana da yara mata guda uku. Ta auri mijinta dan kasuwa Jimmy Davies, bayan an gama auren sai daga baya ta auri Dr Tosin Ajayi. Ajayi ta tabacin gasar yau a makarya ne.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]