Hukumar Jarabawa ta Kasa (Nijeriya)
Hukumar Jarabawa ta Kasa | |
---|---|
Bayanai | |
Gajeren suna | NECO |
Iri | ma'aikata |
Used by | |
Tarihi | |
Ƙirƙira | ga Afirilu, 1999 |
neconigeria.org |
Hukumar Jarrabawa ta kasa (wadda aka fi sani da NECO) ƙungiya ce ta jarabawa a Najeriya wacce ke gudanar da jarrabawar Sakandare da kuma babban satifiket na shaidar ilimi a watan Yuni/Yuli da Nuwamba/Disamba.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Tsohon shugaban ƙasa Abdulsalami Abubakar ne ya ƙirƙiro NECO a watan Afrilu shekara ta 1999.[1] Ita ce ƙungiya ta farko ta Tarayya da ta ba da tallafin rajista ga masu neman ilimi a Najeriya.
Wajibi
[gyara sashe | gyara masomin]Hukumar ta NECO dole ta ɗau nauyin ɗaukar ɗawainiyar hukumar auna ilimi ta kasa (NBEM). Jarabawar farko anyi ta ne a tsakiyar shekara ta 2000.[1]
Gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Lokacin da Abubakar M. Gana ya ke jagorantar ƙungiyar, wanda shugaban ƙasa ya naɗa shi a ƙarƙashin doka mai sashe na 9 (1) na dokar kafa ƙungiyar.[2] Tana da sassa shida, kowane sashe na da darekta mai jagorancin sashen. Haka-zalika kowane Sashe yana da sassa, wanda ya ƙunshi rukuni. Tawagar daraktoci da masu rejista sune hukumar da ke ƙarƙashin jagorancin shugaba Abubakar Mohammed.[3]
Senior Secondary Certificate Examination (internal and external)
[gyara sashe | gyara masomin]Najeriya na ba da ilimi na farko na shekaru shida, karatun karamar sakandare na shekaru uku, karatun sakandare na shekaru uku da karatun gaba da sakandare na shekaru hudu. Darussan Lissafi da harshen Ingilishi wajibi ne kodayake ƙila ba za a buƙaci ilimin lissafi ba don wasu darussa a manyan makarantu.
Basic Education Certificate Examination (BECE)
[gyara sashe | gyara masomin]Basic Education Certificate Examination (BECE) ita ce babbar jarrabawar da za a yi don samun cancantar shiga makarantun sakandare da na sana'a a ƙasashen Ghana da Najeriya. Ana rubuta jarabawar bayan shekaru uku na sashen ƙaramar makarantar sakandarnko shekaru ukkun farko na makaranta sakandare-(Junior section 1, 2, 3).
Jarrabawar Shiga Kasa baki daya
[gyara sashe | gyara masomin]Jarabawar Shiga gama-gari ta ƙasa ana yi wa ɗaliban da suka cika shekara ta 6 a matakin farko na ilimi don shiga Kwalejin Unity na Tarayya. Ana gudanar da jarrabawa biyu a shekara.[4]
A ranar 15 ga watan watan Yulin 2013 ne aka yi ta rade-radin cewa akwai shirye-shiryen da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi na cire Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) daga tsarin ilimin Najeriya saboda karancin da matsakaitan kaso daga ƴan takara a fadin jihohi a Najeriya. Gwamnati ta yi gaggawar karyata waɗannan iƙirari ta hannun ministan ilimi na lokacin Mista Nyesom Wike.[5]
Tsarin Jarrabawar
Tambayoyin Jarabawar Jama'a ta Ƙasa sun ƙunshi kamar haka:
- JARABAWA I
- Sashe na A - Lissafi da Kimiyya na Gabaɗaya-(General Science)
- Sashe na B - Turanci da Nazarin zamantakewa
- JARABAWA II
- Sashe na A – Quantitative da Vocational Aptitude
- Sashe na B – Verbal Aptitude
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "National Examinations Council (NECO): Introduction". Neconigeria.org. 2003-10-30. Retrieved 2014-05-14.
- ↑ NECO official website
- ↑ "FG Constitutes Boards of FMBN, FCDA, NECO, SON, Others, Articles". Thisday Live. 2013-01-01. Archived from the original on 2014-04-07. Retrieved 2014-05-14.
- ↑ "NECO Administrative Structure". Neconigeria.org. 2003-10-30. Retrieved 2014-05-14.
- ↑ "No plan to scrap NECO, UTME, Minister tells Senate". Vanguard News (in Turanci). 2013-04-18. Retrieved 2021-05-27.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Official website
- NECO Job Portal Archived 2021-10-17 at the Wayback Machine
- NECO Result Portal Archived 2023-04-22 at the Wayback Machine
- List Of NECO Office Address Nationwide Archived 2023-04-22 at the Wayback Machine
- How to check NECO Result