Hukumar Labarai ta Najeriya
Hukumar Labarai ta Najeriya | |
---|---|
Bayanai | |
Gajeren suna | NAN |
Iri | news agency (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Hedkwata | Jaguar Abuja |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1976 |
nannewsngr.com |
Da turanci News Agency of Nigeria (NAN), Hukumace mai tace labarai da rahotanni na kasa baki ɗaya wanda gwamnatin tarayyar Nijeriya ke gudanar da ita kaman dai tashan telebijin na NTA.[1] An kuma kafa NAN ne daga cikin wasu dalilai don yada labarai a yankunan daban daban na kasa da kuma yankunan wajen Najeriya kuma don ta zama hanya na daƙile labarai na ƙarya game da Najeriya.[2]
An kafa hukumar ne a 10 ga watan Mayun shekarata 1976, kuma an fara gudanar da aiki a 2 Oktoba 1978 .[3] A Manajan Daraktan na Agency ne Dame Oluremi Oyo.(OON).
NAN na gabatar da labaranta ga masu kallo a kanun labarai guda uku a duk rana. Sashin yanar gizo na hukumar itace www.nannews.ng (a baya can www.nan.ng) wanda aka gabatar a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2016 don watsa labarai a duk fadin duniya musamman ga masu ra'ayin sauraren labarai game da Najeriya, kasar da tafi kowacce kasa yawan jama'a a Afirka.
Hukumar na da dumbin manema labarai da dama a sassa daban daban na kasar suna samo labarai masu mahimmanci daga tushen gaskiya wanda gidajen jaridu na kasa da na yankuna ke wallafawa musamman wadanda basu iya samun labarai a ko ina a fadin kasa.[4] Akwai kudade da ake biya kafin a samu irin wadannan labarai.[5]
Shekarun ritaya daga NAN
[gyara sashe | gyara masomin]Mista Bayo Onanuga, Darekta mai kula da harkokin NAN, ya buƙaci ƙarin yawan shekarun ajiye aiki ga ma'aikatan NAN daga shekaru 60 zuwa shekaru 70. Bayo yayi wannan kira ne a yayin bikin ajiye aiki na Mataimakin babban jami'i a hukumar. Dangane da ra'ayinsa, ma'aikatan jarida na samun ƙwarewa na musamman a lokacin da suka tsufa, inda ya buƙaci ƙungiyoyi da ke da alhaki da su daukaka al'amari zuwa hukumomin da suka dace. Ya kamata a kara yawan shekarun ajiye aiki ga 'yan jarida don basu daman bada gudummawa ga ma'aikatunsu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ahmed, Amir. "Saudi Arabia turns back 1,000 female pilgrims from Nigeria." CNN. Friday 28 September 2012. Retrieved on 29 September 2012.
- ↑ Babatunde Abdulfatai & May 2004, p. 22.
- ↑ "Who Are We? Archived 2012-10-08 at the Wayback Machine" News Agency of Nigeria. Retrieved on 29 September 2012.
- ↑ Babatunde, Abdulfatai. "ASSESSING THE USE OF THE SERVICES OF THE NEWS AGENCY OF NIGERIA (NAN) BY NIGERIAN NEWSPAPERS".
- ↑ "Subscription to News Agency of Nigeria (NAN)"
Mahaɗa
[gyara sashe | gyara masomin]- official website Archived 2014-06-08 at the Wayback Machine