Ikeja Cantonment
Ikeja Cantonment |
---|
Ikeja Cantonment wani katafaren sansanin Sojojin Najeriya ne da ke yankin arewacin Legas. Tana nan daga arewaci tsakiyar gari kusa da gundumomin Isolo da Onigbongo.[1]
Ƙisan kiyashi
[gyara sashe | gyara masomin]A yayin juyin mulki da aka yi a Nijeriya a shekarar 1966 na 28-29 ga Yuli, 1966, Lt. Col. MO Nzefili ya ce an samu rahoton kisan kiyashi a sansanin.[2]
Ta zamo gida ga 9 Brigade na shiyya ta 81 na sojojin Najeriya.
Ajiya
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Janairun 2002, an yi amfani da sansanin don adana "bama-bamai masu girman gaske" da dama, da Sauran Bama bamai da ake burnewa.[3] Da yammacin ranar 27 ga watan Janairu, gobara ta tashi a wata kasuwar titi da ke kusa da sansanin, wadda ita ma gidan iyalan sojoji ne. Da misalin karfe 18:00 da alama gobarar ta bazu zuwa babban kantin sayar da kayan yaki na sansanin, lamarin da ya yi sanadin fashewar makamai a Legas a shekarar 2002 .
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Lagos blasts leave 600 dead". BBC. 28 January 2002. Retrieved 9 October 2008.
- ↑ "Nowa Omoigui. "WITNESSES TO HISTORY: - Lt. Col. M. O. Nzefili (rtd) – Part 2". Retrieved 2020-09-07.
- ↑ Armoury explosion in Lago, Nigeria". World Health Organization. 2002. Archived from the original on May 2, 2003. Retrieved 9 October 2008.
- https://naijaquest.com/list-of-army-barracks-in-nigeria/ - jerin bariki a Najeriya