Ikoro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ikoro
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na slit drum (en) Fassara
Hornbostel-Sachs classification (en) Fassara 111.243

Ikoro kayan kida ne da Igbo na Najeriya suka kirkira kuma suke amfani dashi. Ganga ce ta tsaga da ake bugunta da sanda ko sanduna kuma ana iya amfani da ita a wasu sassan kasar Igbo domin mu'amala, kamar ganguna na magana. Ikoro a kasar Igbo ba kowa ne ya buge shi ba. Yana da matukar muhimmanci a duk lokacin da aka ji kararsa mutane za su taru a dandalin kauye. Da zarar an yi sauti,mutanen da ke kusa da su suna zaton cewa wani abu daga cikin wadannan ya faru:kisan kai, an ƙazantar da ƙasa, an barkewa da yaki, bala'i ya fada cikin al'umma da dai sauransu. Abun da ba makawa da ke faruwa a duk lokacin da aka ji karar Ikoro shi ne jama’a su taru a dandalin kauye domin jin ci gaban da aka samu. Ikoro kuma yana kawo ma'anar gaggawa. Bambancin Ikoro da Ekwe shine girman. Ekwe karami ne kuma mai ɗorewa alhalin Ikoro yana da girman gaske,mutum ɗaya ba zai iya ɗaukarsa kuma ba a taɓa ɗauka daga wuri zuwa wuri.Ana ajiye Ikoro a wani tsayayyen wuri yawanci a filin kauye. Ekwe dai kayan kida ne na yau da kullun kuma ana amfani da shi wajen kunna wakokin gargajiya iri-iri.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

  • Error in Webarchive template: Empty url.