Inumidun Akande
Inumidun Akande | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 10 ga Yuni, 1947 (77 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Sana'a | |
Sana'a | Lauya |
Inumidun Akande[1] An haife ta a ranar 10 ga watan Yuni a shekarar 1947 masaniyar shari'a ce yar Najeriya kuma tsohuwar babban alkalin jihar Legas.[2][3]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi makarantar firamare ta Holy Trinity da ke Ebute Ero, babban birnin jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya kafin ta wuce makarantar Grammar ta Ijebu Ode a jihar Ogun a Najeriya, inda ta samu takardar shedar makarantar West Africa a shekarar 1966. Ta samu digirin farko a fannin shari'a.[4] daga Jami'ar Legas a 1970. Ta kammala karatun lauya a Najeriya a 1971 kuma ta samu Call to Bar a ranar 16 ga Yuni, 1971.[5]
Aikin lauya
[gyara sashe | gyara masomin]Ta shiga aikin shari’a a jihar Legas a farkon shekarun 1970, sannan ta yi aiki a ma’aikatar [6]shari’a a matsayin darakta mai tsara dokoki, kafin ta samu canjin sheka zuwa majalisar dokoki ta kasa, Legas a matsayin mataimakiyar shugabar shari’a a shekarar 1983. An nada ta a benci na Legas. 8 ga Agusta, 1989. An nada ta Babbar Alkalin Jihar Legas a ranar 8 ga Satumba, 2009, shekaru biyu bayan Babatunde Fashola, Gwamnan Jihar Legas ya hau karagar mulki. Inumidun ta yi ritaya daga aiki ne a ranar 10 ga watan Yuni, 2012, tana da shekaru 65 a duniya, inda Ayotunde Phillips ya gaje ta a matsayin babban alkalin jihar Legas na 14.[7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Inumidun_Akande
- ↑ https://archive.today/20150426123618/http://www.thenationonlineng.net/2011/index.php/mobile/society/50216-%E2%80%98she-came,-she-saw,-she-conquered%E2%80%99.html
- ↑ "Justice Inumidun Akande - P.M. NEWS Nigeria"
- ↑ https://books.google.com/books?id=sZ1XAAAAQBAJ&q=Inumidun+Akande&pg=PT181
- ↑ http://www.pmnewsnigeria.com/tag/justice-inumidun-akande/
- ↑ http://www.channelstv.com/2012/06/09/justice-akande-retires-as-chief-judge-of-lagos-state/
- ↑ http://saharareporters.com/2013/11/11/seven-nigerian-judges-targets-efcc-corruption-probe
- ↑ https://archive.today/20150426123613/http://nigeriannotables.com/?p=1111