Ismaila Gwarzo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ismaila Gwarzo
Director General of the State Security Service of Nigeria (en) Fassara

ga Yuni, 1986 - Satumba 1990
Rayuwa
Haihuwa Gwarzo
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara

Ismaila Gwarzo tsohon jami’in tsaro da leken asiri ne a Najeriya. Ya kasance dan sanda, kuma darakta na farko a Hukumar Tsaro ta Jiha; Ministan harkokin 'yan sanda kuma ya kasance mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro a lokacin Sani Abacha.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Aliyu Ismaila Gwarzo a ƙauyen Gwarzo da ke jihar Kano, kimanin kilomita 72 daga babban birnin Kano. Ya shiga rundunar 'yan sanda ta Najeriya inda ya rike mukamai da dama na kara daukar nauyi, ya yi ritaya da babban mukami.

A watan Yunin 1986 shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida ya nada Gwarzo Darakta Janar na sabuwar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), da ke da alhakin leken asirin cikin gida. Mataimakin Daraktan shine Laftanar Kanal A.K. Togun

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://www.xyz.ng/en/people/ismaila-gwarzo-biography-fact-career-awards-net-worth-and-life-story-104254[permanent dead link]