Jibril Gaini
Appearance
Jibril Gaini shi ne mai wa'azin tafarkin addinin Mahadanci ne wanda ya rayu a zamanin Sarkin Zailani (1882-1888) na Masarautar Gombe.[1] Ya kasance mai kishin addini, wanda ya yi nasarar kafa daularsa a Burmi da ke kan iyakar Gombe da Fika.[2] A cikin wadannan lokuttan, guguwar Mahadanci tayi karfi kuma ta mamaye masarautun yammacin Sakkwato da kuma Masarautar Gombe ta gabas. Gaini ya yi tsayin daka na tsawon shekaru a kan hare-hare daga sojojin Masarauntar Gombe da masarautun da ke makwabtaka da su kamar Sakkwato, sannan daga karshe kuma Kamfanin Royal Niger na Biritaniya ta yi nasarar a yakarsa har ya zamo dan gudun hijira a shekarar 1902.