Kachiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kachiya
Description (en) Fassara
Iri ablation (en) Fassara, genital modification (en) Fassara, medical procedure (en) Fassara
removal (en) Fassara
Identifier (en) Fassara
MedlinePlus 002998
eMedicine 002998
MeSH D002944

Kachiya ko shayi wata al'ada ce ko al’amari ne da addinin musulunci ya halarta wadda

ake yanke wani sashe daga al’arran namiji. Wanzamai aka fi sani da aikikn chiya kuma ba kowane wanzami ya iya aikin ba, mafi akasari ma sai wanda yayi gado kuma aka horar dashi sosai.[1]

Karin Bayani Akan Kaciya[gyara sashe | gyara masomin]

Mafi akasari anfi yin kaciya ne lokacin sanyi, kuma a al’adance ana yi ne lokacin da yaro ya kai shekara “bakwai” amma yakan wuce hakan a wasu lokutta, sannan akan boye wa yaro ranar kaciya domin kar ya gudu. A ranar kaciya wanzami zai zo da sassafe, za a kamo yaro a rike shi gam, mahaifin yaro zai gina rami za a zaunar da yaro cillarsa na saitin ramin, sannan a rufe masa idanu a rike shi da kyau don kada ya motsa idan ya ji zafi. Wanzami zai rike cillar ya yi alamar inda zai yanka, idan aka yanke naman, sai abar jinin ya zuba a ramin, sannan a sanya garin magani, kuma a nade ta da auduga. Bayan an gama wanzami zai umurci mai kula da dan kaciya kan ire-iren abincin da za a rika ba shi, kuma za a raba yaro da sauran yara wajen barci kuma ya rika kwanciya a bayansa.[1]

A al’ada akan yi wa dan kaciya wake-wake na tsokana har zuwa lokacin da zai warke. Sannan akan biya wanzami kudi daidai gwargwadon wadatar iyaye.[1]

Addini[gyara sashe | gyara masomin]

Al'amarin shayi ko kaciya ba wai iya mabiya addinin Muslunci ne kadai ke yin shayi wa 'ya'yansu ba. Al'amari ne da ya shafi dukkan 'dan adam. Ma'ana ko wadanne irin mabiyan addini a duniya gabaki daya suna yi wa 'ya'yayensu (maza) kaciya.

Bugu da kari akan yi wa jarirai ne kaciya. Wasu kuma sai idan yaransu sun dan tasa.

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. ISBN 978-169-097-6. OCLC 489903061.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. I. Yahaya., Daura, B.. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. p. 29-30 ISBN 978-169-097-6.