Kaka Mallam Yale

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kaka Mallam Yale
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Borno Central
Rayuwa
Haihuwa Konduga, ga Janairu, 1953 (71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party

Kaka Mallam Yale Ɗan majalisar dattawan Najeriya ne wanda aka zaɓa domin wakiltar jam'iyyar ANPP a jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2007.[1]

Fage[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kaka Mallam Yale a watan Janairun shekarar alif 1953, a garin Yale da ke gundumar Konduga . A shekarar alif 1982, ya yi karatu a Jami’ar Maiduguri inda ya yi Diploma a fannin Gudanarwa (DPA). Ya yi karatun BSc a fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Maiduguri a shekarar 1990.

Alhaji Kaka Mallam Yale ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati a mukamai daban-daban, kuma a shekarar alif 1994, ne gwamnatin soja ta nada shi shugaban karamar hukumar Konduga . An zaɓe shi shugaban karamar hukumar Konduga daga shekarar alif 1999 zuwa 2002. A mataki na jiha ya rike mukamai a sassa daban-daban, ciki har da kasancewarsa shugaban gidan rediyon Borno kadai.

An zaɓe shi a majalisar wakilai ta kasa, mai wakiltar mazabar Konduga, Mafa da Dikwa a matsayin dan jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar alif 1998, amma kwacewar sojoji ya hana shi zama. A watan Satumbar shekarar 2005. ya zama Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno.[2]

Aikin majalisar dattawa[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Borno a Najeriya

An zaɓi Kaka Mallam Yale a matsayin dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar mazaɓar Borno ta tsakiya a shekarar 2007, inda ya tsaya a jam'iyyar All Nigeria People's Party (ANPP). An nada shi a kwamitocin Sojoji, Harkokin Cikin Gida, Kuɗi, Kafa & Sabis na Jama'a da Ilimi[1] A matsayinsa na Sanata, bai ƙaddamar da wani kudiri ba, amma a wasu lokuta yana ba da gudummawa ga muhawara.[3]

Ba a ganinsa a matsayin babbar murya ga mazaɓar sa.[4]

A wata hira da aka yi da shi a watan Agustan shekarar 2008. ya kare jam’iyyar ANPP, amma ya ce abin takaici ne cewa ANPP ta shiga gwamnatin hadin kan kasa maimakon zama jam’iyyar adawa ta gaskiya.[5] A cikin watan Disamba na shekarar 2008, ya soki Kamfanin Mai na Najeriya, yana mai cewa ba su da fasahar gano mai a cikin tafkin Chadi, kuma ya ba da shawarar a bai wa kamfanoni masu zaman kansu aikin.[6]

Ana kallonsa a matsayin wanda zai maye gurbin gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff a zaben shekarar 2011. amma ya kasa cimma hakan.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 https://web.archive.org/web/20080607075208/http://www.nassnig.org/senate/member.php?senator=37
  2. https://web.archive.org/web/20110717202057/http://www.kanuri.net/borno_personalities2.php?aID=65
  3. https://allafrica.com/stories/200905250350.html?page=2
  4. https://web.archive.org/web/20090728063205/http://www.tribune.com.ng/24072009/politics.html
  5. https://sunnewsonline.com/webpages/politics/2008/aug/27/politics-27-08-2008-002.htm[permanent dead link]
  6. https://allafrica.com/stories/200812120169.html
  7. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2011-10-08. Retrieved 2023-03-23.