Kaza
Kaza | |
---|---|
Scientific classification | |
subspecies (en) ![]() | Gallus gallus domesticus ,
|
General information | |
Tsatso |
chicken breast (en) ![]() ![]() ![]() |
Kimanin bugun zuciya |
275 beats per minute (en) ![]() |
![]() |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
![]() |


Kaza wata tsuntsuwa ce na daga cikin jinsin tsuntsaye wadanda. ake ajiyewa a gida domin kiwo. Mutane nayin kiwon kaji ne domin amfana da naman su ko kuma kwansu ko kuma don a sayar domin kudi. Kaza tana yin kwanta dakanta ta kuma ta kyankyashe kayan ta ba kamar wasu nau'in tsuntsaye ba, da basa iya kyankyashe kwansu. Namijin kaza shine ake kira da zakara mace kuma ana kiranta da kaza. Akwai kazan Hausa akwai kazan Bature Wanda inji ke kyankyashe su. Sannan akwai kazan fulani irin wacce fulani suke kiyo, girman kajin fulani ya banbanta da sauran kaji saboda yadda fulani suke kiwon nasu. Har ila yau kaza dai nama ce mai farin jini wajen mutane saboda naman kaza ya banbanta da sauran naman tsinsaye. Naman kaza yana daya daga cikin namar da akafi ci a duniya.
Ita kaza tanada baiwar kyenkyeshe kwayayen ta,ammah wasu hallitu tsuntsaye irin su zabbi, talatalo, har da Agwagwa takan kyenkyeshe kwana su idan an sanya mata. Har ila yau kaza tana kan gaba acikin tsuntsaye da akafi siya a duniya, kuma da akafi ci saboda dadinta da kuma wasu sinadarai da yake tattare da ita.



Rabe raben kaloli na kaji[gyara sashe | gyara masomin]
Akwai kala kala acikin jinsi na kaji kamar baka, fara, ja, sai kuma masu hade da kaloli kamar mai ja da baki dama wani ratsi na fari ko shudi, ko kuma mai digo na fari da baki a dukkan jikinta. Akwai kuma nau'in kaza da ake kira nama wuya wanda zaka gansu babu gashi a wuyan su.

Kalli hotunan Kaji[gyara sashe | gyara masomin]
-
-
-
-
-
-
-
-
-
-
-
-
Kwayayen kaji