Kenneth Matengu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kenneth Matengu
Rayuwa
Haihuwa 1978 (45/46 shekaru)
ƙasa Namibiya
Karatu
Makaranta University of Namibia (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Malami
Wurin aiki Windhoek
Employers University of Namibia (en) Fassara

Kenneth Kamwi Matengu (an haife shi a shekara ta 1978 a Katima Mulilo, Namibia) farfesa ne na ƙasar Namibiya kuma mataimakin shugaban jami'ar Namibia tun daga shekarar 2018 bayan ya maye gurɓin Farfesa Lazarus Hangula mai ritaya a watan Agusta 2018. Ya kasance Pro-Vice Chancellor for Research, Innovation and Resources Mobilization a Jami'ar Namibia daga shekarun 2016 zuwa 2018. [1] A ranar 29 ga watan Yuni 2018, an naɗa Matengu a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Namibia na uku ya zama mafi karancin shekaru da ya karɓi muƙamin. [2] [3] [4] [5] [6]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Matengu ya yi makarantar sakandare a Caprivi Senior Secondary. Yana da Certificate in International Relations daga Jami'ar Tampere, Digiri na farko a Geography da Sociology daga Jami'ar Namibia, da Dakta na Falsafa, Ph.D (exemia cum laude) a Innovation Diffusion and Development daga Jami'ar Gabashin Finland. Ya wallafa muƙaloli bita na guda 50, littattafai da surori na littattafai, da kuma takaddun taro na duniya. [7] [8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Unam partners with the best Archived 2018-08-10 at the Wayback Machine Namibian Sun
  2. Unam appoints Kenneth Matengu Archived 2018-08-10 at the Wayback Machine The Villager
  3. "Matengu Appointed as UNAM's New Vice Chancellor". Archived from the original on 2018-08-10. Retrieved 2023-12-12.
  4. Who are these people a rundown on unam vc candidate Archived 2018-06-30 at the Wayback Machine New Era Newspaper
  5. Matengu is Unams new VC
  6. Matengu gets Unam top job - Education Namibian Sun
  7. Kenneth Matengu Personal Story Cardiff University
  8. UNDP hosts inaugural conference of IGU Commission on African Studies Devdiscourse