Esmevânio Kialonda Gaspar (an haife shi a ranar 27 ga watan Satumba 1997), wani lokaci ana kiransa kawai da Gaspar, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Portugal Estrela.
Gaspar ya fara taka leda tare da kulob din Angolan Sagrada Esperança, inda ya buga wasanni 4. A ranar 1 ga watan Agusta 2022, ya koma Liga Portugal 2 club Estrela. [1]