Kisan kiyashin Zurmi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kisan kiyashin Zurmi

A ranar 11-12 ga watan Yunin shekara ta 2021, an yi kisan kiyashi a Zurmi, Jihar Zamfara, Najeriya.[1] Harin dai wani ɓangare ne na rikicin da ya barke a yankin tsakanin gwamnati da 'yan bindiga.[2]

A ranakun 11 da 12 ga watan Yunin shekara ta 2021, wasu ‘yan bindiga a kan babura sun kai hari a kauyukan Kadawa, Kwata, Maduba, Ganda Samu, Saulawa da Askawa da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashe mutane 53.[1][3] Yawancin waɗanda harin ya rutsa da su manoma ne da aka harbe a lokacin da suke aikin gona.[4]

Bayan haka[gyara sashe | gyara masomin]

Da aka kawo karshen kisan kiyashin, an gano gawarwakin mutane 53 tare da yi musu jana'iza yadda ya kamata. An baza ‘yan sanda a yankin domin hana sake afkuwar wannan kashe-kashen jama’ar.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Gunmen storm villages, kill dozens in Nigeria's Zamfara state | Nigeria News". Al Jazeera. Retrieved 2021-06-27.
  2. "Gunmen attack villages, kill over 90 in Nigeria". Deutsche Welle (in Turanci). Retrieved 2021-12-17.
  3. "Scores Killed In Gruesome Massacre In Zamfara". HumAngle Media (in Turanci). 2021-06-17. Retrieved 2021-12-17.
  4. 4.0 4.1 "Gunmen kill dozens of villagers in Nigeria's restive northern region". TRT World (in Turanci). Retrieved 2021-12-17.