Jump to content

Kiyomizu Temple

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kiyomizu Temple
清水寺
 UNESCO World Heritage Site
Historic Monuments of Ancient Kyoto
Saigoku Kannon Pilgrimage
The Twenty-Fifth Reikyo of Dharan Shonin
[[]]
Shinbutsu Reijō Junpai no Michi
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaJapan
Prefecture of Japan (en) FassaraKyoto Prefecture (en) Fassara
City designated by government ordinance (en) FassaraKyoto
Ward of Japan (en) FassaraHigashiyama-ku (en) Fassara
Coordinates 34°59′41″N 135°47′06″E / 34.994831°N 135.785003°E / 34.994831; 135.785003
Map
History and use
Renovation2008 - 2020

Increase 798

Reconstruction 1633
Addini Kita-Hossō sect (en) Fassara
East Asian Yogācāra (en) Fassara
Suna Thousand-Armed Thousand-Eyed Avalokiteśvara (en) Fassara
Karatun Gine-gine
Style (en) Fassara kakezukuri (en) Fassara
Yawan fili 12.3 ha
Muhimman Guraren Tarihi na Duniya
Criterion (ii) (en) Fassara da (iv) (en) Fassara
Reference 688-004
Region[upper-roman 1] Asia and Oceania
Registration )
Offical website
  1. According to the UNESCO classification
hoton kiyomizu

Kiyomizu Temple wajen bautar Buddhizanci da ke birnin Kyoto, kasar Japan. Wurin bautar na daga cikin wuraren tarihi na tsohuwar Kyoto (biranen Kyoto, Uji da kuma Otsu) na UNESCO.[1]

An kafa wurin bauta na Kinyomizu a zamanin Heian.[2] Ya zuwa shekarar 778, wurin ya kasance mallakin Budha Kita-Hosso a karkashin Enchin Shonin. Ya kasance firisti daga Nara (babban birnin Japan daga 710 zuwa 784), wanda akai wa wahayi cewa ya gina wurin bautar a gabar kogin Otowa.[3]

Acikin shekarar 798, Shogun Sakanoue no Tamuramaro ya kara bunkasa wurin bautar ta hanyar sanya wani katafaren dakin taro wanda aka shirya daga fadar Sarki Kammu (r. 781–806). Sarkin ya bar garin Naru a dalilin tsananin ikon da malaman addinin Budha ke da shi akan gwamnatin garin. A wancan lokacin, akwai adawa mai tsanani a tsakanin wurin bautar Budhanci na Kofuku-ji da kuma wurin bauta na Kiyomizu, wanda dukkansu suna da tsananin karfin iko a yankin.[3]

Ginin wurin bautar na yanzu an yi shine a shekarar 1633, wanda Tokugawa Iemitsu ya bayar da umurnin yin ginin.[4] Ba ayi amfani da ƙusa ko daya ba a wajen yin ginin. Ta samo sunanta ne daga wani kogi mai kwarara zuwa sashin tuddai na yankin -wato waterfall a yankin. Kiyomizu na nufin ruwa mai haske ko ruwa mai kyau ko tsafta.[5][6]

Tun asalin wurin bautar tana da alaka da Hossō daga lokacin Nara.[7] Amma an raba wannan alakar a shekarar 1965, masu daukan nauyin wurin bautar na yanzu suna kiran kansu da suna mambobin sashin "Kitahossō".[8]

Wurin bautan yana dauke da sauran dakunan bauta da dama, daga cikinsu akwai dakin bauta na Jishu, wanda aka sadaukar don Ōkuninushi, ubangijin soyayya da kuma "kyawawan hadi" - na soyayya.[9] Acikin dakin bauta na Jishu akwai "duwatsun soyayya" guda biyu wanda aka ajiye da nisan mita 10 (30 feet) a tsakaninsu, wanda baki masu fama da kadaici zasu zagaya idonsu rufe. Cin nasara shine isa zuwa wajen dayen dutsen da idanu rufe, wannan na nufin cewa masu ziyara zasu cin ma samun soyayya ko kuma soyayya ta gaskiya.[10] Za'a iya taimkawa mutum wajen yin tafiyar, har ila yau, abokin soyayyar mutum zai iya raka shi.

Ana gudanar da tsubbace-tsubbace da hayaki da kuma rufa ido - omikuji (fadan abunda zai faru a gaba ta takarda) a wajen bautan. Wannan wurin bauta yafi shahara a lokacin bukukuwa (musamman zagayowar Sabuwar Shekara da kuma bikin obon wanda akeyi a lokacin rani), a lokacin da ake samun sabbin baki kuma ana sayar masu da kayan gargajiya.[11]

A cikin shekara ta 2007, Kiyomizu-dera ya shiga cikin zabi 21 don zama daya daga cikin sabbin wuraren al'ajabi guda bakwai na duniya,[12] amma ba'a zabe shi ba a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi guda bakwai da suka lashe gasar. An lullube ginin da wani abu mai shara-shara a yayinda ake gyara ta don Wasannin Olympics ta 2020.

Tsarin gini

[gyara sashe | gyara masomin]

Wurin bautan na nan a yankin tuddan Mount Otowa, a sashin dutsen Higashiyama mountain wanda ya mamayen yankin gabashin Kyoto. Babban dakin yana dauke da katafaren baranda, da dogayen ginshikai, wanda ya fito ta saman tuddai kuma ya bada sura mai kyawun gani. An gina manyan barandu da manyan dakunan taro a zamanin Edo, don tarbar masu zuwa buta da dama.[13]

A karkashin babban dakin bautan akwai Otowa waterfall, inda hanyoyin ruwa guda uku ke shiga cikin wata korama. Baki kan tarbi ruwan su sha wanda ake tsammani yana ikon sanya buruka su zamo gaskiya. Akwai kuma Tainai Meguri, wani dogon kogo mai duhu wanda akace yana wakiltar tumbin bodhisattva Mahāpratisarā.[14][15]

Kara bincike

[gyara sashe | gyara masomin]

Samfuri:Portal

  1. "Historic Monuments of Ancient Kyoto (Kyoto, Uji and Otsu Cities)". Retrieved 2008-12-20.
  2. Ponsonby-Fane (1956), p. 111.
  3. 3.0 3.1 "Kiyomizu-dera". World History Encyclopedia (in Turanci). Retrieved 2022-07-11.
  4. Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 37
  5. "Kiyomizu Temple". 2007-04-07. Archived from the original on 2009-04-03. Retrieved 2008-12-18.
  6. "Kiyomizudera, Kyoto". Archived from the original on 2009-09-12. Retrieved 2008-12-18.
  7. Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 32
  8. "Kiyomizu-deploy". Archived from the original on 2017-11-15. Retrieved 2023-06-16.
  9. "Kiyomizu Temple". 2007-04-07. Archived from the original on 2009-04-03. Retrieved 2008-12-18.
  10. "japanvisitor.com". Retrieved 2010-08-21.
  11. "Kiyomizu-dera Temple". Archived from the original on December 10, 2008. Retrieved 2008-12-20.
  12. "The Finalists for The Official New 7 Wonders of the World". Archived from the original on 2009-06-01. Retrieved 2009-06-01.
  13. Graham, Patricia J. (2007). Faith and Power in Japanese Buddhist Art. Honolulu: University of Hawaii Press. ISBN 978-0-8248-3126-4. p. 80
  14. Mukri, Farha (3 April 2019). "From darkness to light at Japan's Kiyomizu-dera". The Hindu. Retrieved 2023-02-12.
  15. "Kiyomizu-dera temple is one of Kyoto's must-see attractions!". 13 June 2016.