Kogin Mbridge

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Mbridge ko Mebridege kogi ne a arewacin Angola.Bakinsa yana Tekun Atlantika kusa da garin N'Zeto a lardin Zaire.Asalinsa yana kusa da birnin Cuimba, kuma ya kasance wani yanki na iyaka tsakanin lardunan Zaire da Uige. Rarrabansa sun hada da Lufunde, da Lucunga, da Luqueia, da Lufua.

Ana sa ran kammala ginin gada akan kogin kusa da N'Zeto a karshen shekarar 2013.[1]

An nuna bakin kogin da yashi a kan tambarin 2008 da Angola ta fitar.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin kogunan Angola

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]