Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
National Union of Nigerian Students
students' union (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1956
Ƙasa Najeriya

Kungiyar Dalibai ta Kasa (NUNS) kungiya ce ta dalibai da ta haɗa daliban Najeriya a cikin Najeriya da kuma ƙasashen waje.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa kungiyar NUNS a cikin shekarar 1956, bayan sauye-sauyen tsari a cikin Ƙungiyar Dalibai ta Yammacin Afirka. Ƙungiyar ta haɗa majalisar dalibai a Ife, Zaria, da Nsukka.[1]

A cikin watan Afrilun 1978, ɗaliban Najeriya sun fuskanci ƙarin kuɗaɗen makarantu, kuma haɗaɗɗiyar kungiyar NUNS da ta haɗa da jami'o'i a faɗin ƙasar sun halarci zanga-zangar; Ali Must Go. Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar tura sojoji da 'yan sanda, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai sama da ashirin ko kuma suka samu munanan raunuka. An rufe jami'o'i uku kuma an dakatar da NUNS. An sallami wasu ma’aikatan Jami’a da dalibai da dama.[2]

Kowane shugaban ƙungiyar yana da wa'adin shekara 1 kuma shugaban da aka zaba a ranar 4 ga Satumba shi ne Umar Faruq Lawal.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "National Union of Nigerian Students (NUNS)". Facts On File. Retrieved 13 December 2013.
  2. Coutsoukis, Photius. "Nigeria Student Organizations". Retrieved 13 December 2013.
  3. "Nans presidential election". Vanguard news.