Kunle Soname

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kunle Soname
Rayuwa
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar Lagos
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Kunle Soname ɗan siyasar Najeriya ne, ɗan kasuwa, mai sha'awar wasanni kuma shugaban Bet9ja, gidan yanar gizon caca da ya kafa a cikin shekarar 2013. Shi ne kuma ɗan Najeriya na farko da ya sayi kulob ɗin Turai CD Feirense wanda ya saya a cikin shekarar 2015.[1][2] Shine wanda ya kafa kamfanin jirgin sama mai zaman kansa na Najeriya ValueJet (Nigeria)[3][4]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Soname ya karanta Estate Management a jami'ar Obafemi Awolowoinda ya kuma kammala a cikin shekarar 1988.[5] Ya kuma shiga siyasa a shekarar 2003 kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban zartarwa na ƙaramar hukumar Ikosi-isheri muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2011.[6][7]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Remo Stars wacce aka fi sani da FC DENDER Soname ce ta kafa a cikin shekarar 2004. Daga nan ne aka mayar da kulob ɗin daga Jihar Legas zuwa yankin Remo na Jihar Ogun, kuma a yanzu yana buga gasar firimiya ta Najeriya mafi girma.

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Soname ya auri Kemi Soname kuma suna da ɗiya Erioluwa.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]