Kunun tsamiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kunun tsamiya
Kayan haɗi tsamiya, gero, sukari, peppercorn (en) Fassara da citta

Kunun tsamiya dai daya ne daga abincin Bahaushe a kasar Hausa wanda akasari aka fi amfani da shi ko in ce aka fi shan sa da zarar hantsi ya dubi ludayi lokacin walaha (hantsi) mafi lokuta yayin aikin gona, bikin aure, suna kai har ma da makwalla-makwalla. Kunun tsamiya dai abin sha ne mai kauri wanda ake yin sa da garin gero, tsamiya da tafasasshen ruwa.Ana yi masa gaya ta hanyar kwaba garin ya yi dan tauri-tauri sai a jefa cikin tafasasshen ruwan nan. Bayan an kuma kwaba garin da jikakken ruwan tsamiya, sai a zuba shi a masaki (kwarya-babba) a dama shi ruwa-ruwa, kauri-kauri, sai a kawo wannan tafasasshen ruwan na kan wuta a zuba a cikin damammen garin nan mai ruwan tsamiya sai a juya da babban ludayi za a ga ya yi kauri kirtib. Shi ya Kuma ya sa Bahaushe yake yi masa take da cewa kunu na tsula tsafin mata.[1][2][3][4].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.yaurimedia.com.ng/2019/01/gero-gargajiyance-b.html[permanent dead link]
  2. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  3. https://cookpad.com/ng/recipes/6557695-kunun-tsamiyatamarind-pap
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-31. Retrieved 2020-12-27.