Kura (dabba)
Kura (dabba) | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | mammal (en) |
Order | Carnivora (en) |
Superfamily | Herpestoidea (en) |
dangi | Hyaenidae Gray, 1821
|
Geographic distribution | |
Kura jam'in ta shine kuraye kura wata dabba ce mai launin kasa-kasa ko kuma ratsi-ratsi mafarauciyar nama (abincinta) tana daga cikin dabbobin daji masu hatsarin gaske. Wasu suna ganin kamar kura bata iya farauto abincin ta, sai dai ba haka zancen yake ba. Kura tana daga cikin dabbobin daji masu cin nama Kuma Naman ko wane iri ne ba wai sai dan'uwanta dabbobi ba har mutane takan kashe ta ci naman su. Da kura da zaki da sauran dabbobi masu cin nama dukkan su, suna da hatsarin gaske. Ana kuma kiran kalan wadannan dabbobin da turanci (carnivorous) wato masu cin nama ko wane irine. Sai dai kuma ita kura tana da ban tsoro sannan itama tana da tsoro sosai, ga tsoro ga kuma ban-tsoro sai dai wani abinda baku sani ba game da kura shine, kura tana da basira sosai. Kuraye suna yawo kusan garke-garke, daga biyu zuwa fiye da haka, sai dai wasu masana sun tabbatar da cewa garken kuraye mafi yawa da aka taɓa gani, shine wanda aka gan kuraye saba'in da biyu (72) a garke daya.[1][2][3][4][5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Abubuwan da ba ka sani ba game da kura". bbc hausa. 4 November 2019. Retrieved 6 July 2021.
- ↑ Nicholls, Henry (28 October 2014). "The spotted hyena is not a habitual scavenger, despite what you may have heard, and it is fabulously intelligent to boot". bbc.co.uk. Retrieved 6 July 2021.
- ↑ Ɗalha Taura, Naziru (10 February 2020). "Wata jibgegiyar 'Kura' ta gudu daga gidan 'Zoo' a Imo, an kama ta bayan sa'a 6". legit hausa. Retrieved 6 July 2021.
- ↑ A Ibrahim, Yusha'u (16 October 2020). "Yadda Na Yi Gamo Da Kura A Wajen Neman Kudi —Aminu Dantata". Aminiya dailytrust.com. Retrieved 6 July 2021.
- ↑ Fletcher, Martin (23 February 2014). "The urban hyenas that attack rough sleepers". BBC News. Retrieved 6 July 2021.