Ƙyaure

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Kyaure)
kyaure/kofa a jingine
dakunan kauye wadanda ake sa musu kyaure

kyaure kyaure na nufin marufin daki, wanda a yanzu mafi yawan mutane musamman matasa suka fi sanin shi da kofa. Amma mutanen zamfara da Sokoto suna Kiran kofa da suna Dangarama.[1]

Sunayen Kyaure da Hausa[gyara sashe | gyara masomin]

Ana kuma kiran kyaure da sunaye daban-daban ya danganta da wani yanki ne a Arewacin Najeriya, a kasa sunayen kyaure ne daban-daban:

  1. kyaure wani abune da ake rufe daki dashi tunba irin na kara dinnan ba, musamman Bukka irin dakin Fulani.
  2. Gambu shima ana amfani dashi wajen rufe daki, shi kuma anayinshi da pale-pale na kwano (Zinc) wato rufi.
  3. kofa ita kuma kofa mafi akasari masu walda ke hadata itama dai wajen rufe daki ake amfani da ita. Akwai kofa ta zamani wadda masu kafinta suke yinta.
  4. Dangarama ita Dangarama wani dan tudu ne da akeyi a bakin kofar daki tunba irin na dauri ba.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Definition of kyaure in English". Hausa Dictionary. Retrieved 26 July 2023.