Lépua
Lépua | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Angola, 23 Disamba 1999 (24 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Angola | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Simone Eduardo Assa Miranda (an haife shi a ranar ashirin da uku 23 ga watan Disamba shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da tara 1999), wanda aka fi sani da Lépua, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sagrada Esperança da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Angola.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Lépua samfurin matasa ne na kungiyar kwallon kafa ta Sagrada Esperança, kuma ya wasan sa na farko tare da babban ƙungiyar a cikin shekarar dubu biyu da sha takwas 2018.[1]
Ayyukan kasa da kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Lépua ya fara wasa na farko tare da tawagar ƙasar Angola a rashin nasara da ci ɗaya da nema 1-0 shekarar 2022 na cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a hannun Masar a ranar ɗaya 1 ga watan Satumba shekarar dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021.[2]