Le spectre de Boko Haram

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Le spectre de Boko Haram
Asali
Characteristics
External links

Le spectre de Boko Haram (transl. The Spectrum of Boko Haram) fim ne na ƙasar Kamaru na shekarar 2023 wanda Cyrielle Raingou ta rubuta kuma ta ba da umarni matsayin fim ɗin ta na farko. Fim ɗin ya fara fitowa a duniya a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na 2023 a Rotterdam.[1] Fim ɗin kuma ya lashe lambar yabo ta Tiger a karo na 52 na bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Rotterdam.[2][3][4] Fim ɗin ya nuna mummunan gaskiyar gwagwarmayar yau da kullun na mutanen Kamaru waɗanda dole ne su magance ayyukan rashin mutunci da na zalunci na kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.[5]

Takaitaccen bayani[gyara sashe | gyara masomin]

Shirin fim ɗin ya kunshi wasu yara ‘yan makaranta uku Falta Souleymane da Ibrahim Alilou da kuma Mohamad Alilou waɗanda dukkansu ke da burin rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana duk da hadarin da kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ke da shi da ke ci gaba da barazana ga rayuwar dubban waɗannan mutane dake zaune a Arewacin Kamaru. Falta ta nuna girma da natsuwa yayin da ta tashi daga jimamin mutuwar mahaifinta da 'yan ta'addar Boko Haram suka kashe a yayin da Ibrahim da Mohamad ke ta faman tinkarar al'amuransu na yau da kullum saboda sun yi kasala da abubuwan da suka faru a baya. Duk ’yan’uwan sun rabu da iyayensu.

Shiryawa[gyara sashe | gyara masomin]

An shirya fim ɗin tare da haɗin gwiwar Tara Group na Kamaru da Label Vidéo na Faransa tare da ayyukan haɗin gwiwar da kamfanonin watsa labarai na Faransa Canal+ International da Télé Bocal ke jagoranta. Jarumar fim ɗin Cyrielle Raingou da kanta ta fito daga arewacin ƙasar Kamaru[6] ta bayyana irin abubuwan da ta gani a cikin shirin fim ɗin yayin da kuma ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana halin da talakawan Kamaru ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon halayen Boko Haram.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Le spectre de Boko Haram | IFFR". iffr.com. Retrieved 2023-02-11.
  2. "Le spectre de Boko Haram and Endless Borders are the victors at IFFR 2023". Cineuropa (in Turanci). Retrieved 2023-02-11.
  3. Ross, Rafa Sales (2023-02-03). "'Le Spectre de Boko Haram,' a View of Terrorism Seen Through Children's Eyes, Wins Rotterdam's Tiger Award". Variety (in Turanci). Retrieved 2023-02-11.
  4. "Le spectre de Boko Haram wins the Tiger Award 2023". iffr.com. Retrieved 2023-02-11.
  5. Elfadl, Murtada (2023-02-06). "'Le Spectre de Boko Haram' Review: Living Under the Threat of Violence in Northern Cameroon". Variety (in Turanci). Retrieved 2023-02-11.
  6. "Review: Le spectre de Boko Haram". Cineuropa (in Turanci). Retrieved 2023-02-11.