Lillian B. Allen
Lillian B. Allen | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Lillian Beatrice Allen |
Haihuwa | Winnipeg, 9 Nuwamba, 1904 |
ƙasa | Kanada |
Mutuwa | Victoria (en) , 13 Nuwamba, 1994 |
Sana'a | |
Sana'a | university teacher (en) da mai daukar hoto |
Lillian Beatrice Allen (Nuwamba 9, 1904 - Nuwamba 13, 1994) 'yar asalin Kanada ce, malama kuma mai daukar hoto. An san ta da hotu nan ta waɗan da aka nuna a Jami'ar Manitoba da kuma buga Frost: Hotuna na Lillian Allen a cikin 1990.
Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Allen a Winnipeg, Manitoba, a cikin 1904. Ita ce babba a cikin yara uku na masani yar kimiyyar Kanada Frank Allen (1874 – 1965) da Sarah Estelle.
Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
A 1926 Allen ta sami BA a Liberal Arts daga Jami'ar Manitoba. Daga baya ta karanci fasaha a Winnipeg School of Art, inda ta sami difloma, kuma ta ci gaba da koyar da darussan safiyar Asabar. [1] A 1947 ta sami MSc daga Jami'ar Syracuse .
Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]
..Daga 1934, ta yi lacca a Jami'ar Manitoba kan gidaje da ƙira, a matsayin wani ɓangare na Faculty of Agriculture and Home Economics. Ta yi ritaya a matsayin aboki yar Farfesa a 1971. Ta kuma gabatar da jawabai kan batu tuwa daban-daban. A cikin 1976, ta sami cikakken nunin hoto mai launi, "Ice and Frost" a Langley Centennial Museum . Allen ta kuma yi sha'awar kayan daki na zamani, inda ta buga kasidar ta ta jami'a Nazarin Zane-zanen Kayan da aka Gina daga Sabbin Kayayyaki daga 1925 zuwa 1945 a 1947.
Bayan ta yi ritaya ta ci gaba da aikinta a matsayin mai daukar hoto na yanayi, inda ta buga littafin Frost: Photographs in 1990 ( Hyperion Press : ). An kuma nuna hotu nanta a Jami'ar Manitoba da Makarantar Fasaha ta Winnipeg .
Allen ta kasance mai ƙwazo a cikin ƙun giyar fasaha ta Manitoba, kasan cewarta memba na kwamitin sa kai na Winnipeg Art Gallery kuma tana koyarwa a Crafts Guild na Manitoba . A cikin 1980, ta sami lambar yabo ta "Woman of the Year Award" daga YWCA .
Daga baya rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]
Allen ta koma Victoria, British Columbia a 1981. Takardun Allen suna cikin tarin Jami'ar Manitoba. [2]