Jump to content

Lockdown (2021Nigerian film)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Lockdown fim ne na wasan kwaikwayo mai ban sha'awa wanda akai a Najeriya a shekara ta dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021 wanda Moses Inwang[1] ya rubuta kuma ya ba da umarni. jaruman fim ɗin sun haɗa da Omotola Jalade-Ekeinde, Tony Umez da Charles Awurum a cikin manyan jarumai. [2] An shirya fim ɗin ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Studios Sneeze Films, FilmOne, iFactory Films da CEM Media Group. [3] Fim din ya samo asali ne daga babban likitan Najeriya Ameyo Adadevoh wanda aka yaba da yadda ya dakile yaduwar cutar Ebola a Najeriya ta hanyar sanya mara lafiya, Patrick Sawyer, a keɓe duk da matsin lamba daga gwamnatin Laberiya . Fim ɗin ya fito na wasan kwaikwayo a ranar 28 ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021 kuma ya sami ra'ayoyi daban-daban daga masu suka.

Yin wasan kwaikwayo

[gyara sashe | gyara masomin]

An dage babban daukar hoton fim din saboda dokar hana fita da aka yi a Najeriya a farkon bullar cutar COVID-19 a watan Maris na shekara ta dubu biyu da ashirin 2020. Fim ɗin ya zama kashi na biyu na Asusun Fina-Finan Yammacin Afirka tare da haɗin gwiwar Sneeze Films, FilmOne, iFactory Films da CEM Media Group tare da HuaHua Media da Empire Entertainment. An yi fim ɗin ne bisa bullar cutar Ebola duk da hasashe da aka yi na cewa an yi fim ɗin ne a kan barkewar COVID-19. Darakta, Inwang wanda shi ne ya kirkiro labarin na fim din ya bayyana cewa ya fara daukar labarin ne a shekarar 2016 bisa bullar cutar Ebola a shekarar 2015. [4] An fi yin fim din ne a Legas .

  1. Nwogu, Precious (2021-03-17). "Watch Omotola Jalade-Ekeinde, Sola Sobowale, Tony Umez, Jidekene Achufusi in 'Lockdown' teaser". Pulse Nigeria (in Turanci). Retrieved 2021-07-08.
  2. Tv, Bn (2021-03-18). "Must Watch Teaser: Omotola Jalade-Ekeinde, Sola Sobowale in Moses Inwang's Upcoming Movie "Lockdown"". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-07-08.
  3. "FilmOne to co-produce 'Lockdown' with CEM Media and Moses Inwang". Pulse Nigeria (in Turanci). 2021-03-17. Retrieved 2021-07-08.
  4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1