Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Akwa Ibom

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Akwa Ibom
Bayanai
Iri government agency (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1987

Ma’aikatar lafiya ta jihar Akwa Ibom ita ce ma’aikatar gwamnatin Jihar, wacce ke da alhakin tsarawa, da aiwatar da manufofin Jihar a fannin kiwon lafiya.[1]

An kafa ma'aikatar a matsayin MDA (Ma'aikatar Ma'aikatu, da Hukumomi), a cikin 1987, tare da ƙirƙirar jihar Akwa Ibom ta Najeriya. ma'aikatar na da sassa 7, ko Daraktoci, Kowannensu yana da nasa nauyin da ya rataya a wuyansa ga Ma’aikatar da Gwamnati. Su ne Darakta na ayyukan jinya, Darakta na ayyukan Likita, Daraktan ayyukan Magunguna, Daraktan ayyukan Kiwon Lafiyar Jama'a, Daraktan Tsare-tsare, Bincike, da Ƙididdiga, Daraktan Asusun da Kuɗi, da Daraktan Gudanarwa / Kayayyaki.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Lassa Fever: Akwa Ibom Residents Tasked On Clean Environment • Channels Television". Channels Television. 2016-01-29. Retrieved 2017-02-26.
  2. "Akwa Ibom State Ministry of Health - NGVotes". Archived from the original on 2019-03-06. Retrieved 2019-03-03.