Jump to content

Maƙabarta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maƙabarta
geographical feature (en) Fassara da building type (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara Mutuwa da burial (en) Fassara
Karatun ta necropolis studies (en) Fassara
Hashtag (en) Fassara Friedhof da Cemetery
Manifestation of (en) Fassara Mutuwa da burial (en) Fassara
Maintenance method (en) Fassara grave tending (en) Fassara
makabartar ramle
wata makabartar kirista

Maƙarbata wuri ne da ake bizne ko kuma binne waɗanda suka mutu daga cikin mutane. Wanda aka tanada shi don kawai idan ɗaya daga cikin mutane ya mutu sai aje filin maƙabarta a gina rami kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada ma Al'ummar Musulmi. Idan kuma Kirista ne to sukan binne mamaci akan yadda Addinin kiristanci ya koyar dasu. A Addinin Musulunci zuwa maƙabarta yanada addu'a wato kafin shiga maƙabarta musanman lokacin da aka zo za'a shiga, kuma a Musulunci Mata basa zuwa maƙabarta sai dai Maza ne zasu je su haƙa rami ko gina shi kafin azo da mamaci, duk tun daga haƙa ramin har komai anayi ne a bisa koyarwar musulunci. Wasu maƙabartun zaka ga hada mai gadi, wasu kuma babu mai gadi. Maƙabarta takan cika, to a lokacin da maƙabarta ta cika sai a daina bizne mutane a cikin ta, sai a sake samun wani filin a buɗe sabuwar maƙabarta.[1][2] akan ɗauka mamaci a cikin makara idan maƙabarta na kusa idan kuma bata kusa to bayan an saka mamaci a cikin makara sai kuma asashi a mota don akwai matar maƙabarta musanman, wadda ake amfani da ita wajen kai matattu a maƙabarta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]