Majalisar Lafiya ta Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

World Health Assembly

Bayanai
Gajeren suna WHA
Iri Forum through which the World Health Organization (WHO) is governed.
Mamba na 194 Countries
Mulki
Hedkwata Geneva, Switzerland
Mamallaki Hukumar Lafiya ta Duniya
who.int…
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi taro a zauren Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ( Switzerland ).

Majalisar Lafiya ta Duniya (WHA) wata dandalin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) gudanarwa a karkashin kasashe mambobinta guda 194. Ita ce babbar hukumar kafa manufofin kiwon lafiya a duniya kuma ta ƙunshi ministocin lafiya daga ƙasashe daban daban.

Membobin WHA gabaɗaya suna yin taro a kowace shekara a cikin watan Mayu a Geneva a Fadar Majalisar Dinkin Duniya, inda hedkwatar WHO take. Muhimman ayyukan hukumar ta WHA shine yanke shawara kan manyan tambayoyin siyasa, da kuma amincewa da shirin aiki da kasafin kudin hukumar ta WHO da kuma zaben Darakta-Janar na majalisar (kowace shekara ta biyar) da kuma zabar mambobi goma a duk shekara don sabunta wani bangare na hukumar zartarwa.[1] Muhimman ayyukanta su ne ƙayyade manufofin Ƙungiya, kula da manufofin kuɗi, da dubawa da amincewa da kasafin shirin da aka tsara.

Membobi, masu lura da kuma dokoki[gyara sashe | gyara masomin]

Membobin asali na WHA, a taron farko da aka yi a 1948, ya ƙunshi membobin ƙasashe guda 55. [2] WHA tana da, a halin yanzu, kasashe membobi guda 194 (gabaki daya membobin Majalisar Dinkin Duniya ba tare da Liechtenstein ba, da tsibirin Cook da Niue ).[3][4] Hakanan WHA ta ƙunshi membobin abokan tarayya guda biyu, Puerto Rico da Tokelau. Bugu da kari, akwai hukumomi guda 7 da ke da alhakin lura a WHA, sune Vatican, Hukumar kasar Palastine, Sovereign Military Order of Malta, International Committee of the Red Cross, International Federation of Red Cross and Red Crescent Societies, Kungiyar South Centre, da kuma Inter-Parliamentary Union.

Ana gudanar da majalisar a karkashin tsarin Dokokin Majalisar Lafiya ta Duniya,[5] Babban Kwamitin Majalisar ne ke tsara duk wata ajenda ta kungiyar, wanda ya hada da gungun mutum 25 da ya hada da shugaba guda da kuma ciyomomin rukuni, da kuma sauran wakilai wanda Majalisar da ta gabata ke zaba.[5]

Majalisar zartarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Duk shekara, majalisar tana zaben membobi daga jagororinta don sabunta majalisar zartarwa (Executive Board). Wannan sashe na karkashin kulawa a Babi na IV, Kasida ta 24 zuwa 29, na kundin tsarin mulkin WHO. Dole ne majalisar zartarwar ta kasance tana da daidaito dangane da yankunan duniya, sannan "za'a zabesu na tsawon shekaru uku, kuma ana yi sake sabarsu... sannan majalisar zatayi taro sau biyu a shekara kuma zata zabi inda za ayi taron".[6]

Kudurori[gyara sashe | gyara masomin]

Muhimman kudurori da akayi amfani da su a wajen tsara dokokin WHA sun hada da:

Bugu da kari, WHA ta hanyar kudurorinta ta dabbaka matakan tsare-tsaren WHO da dama da ke da alaka da fannuka daban daban na inganta lafiya a sassa da dama na duniya, irin su;

  • Kawo karshen cutar Agana a duk fadin duniya, wanda aka fara gudanarwa a shekarar 1959, sannan kuma aka sanar cewa an ci nasararta a shekarar 1980[7]
  • Kawo karshen cutar Polio a duk fadin duniya, wanda aka fara gudanarwa a shekarar 1988,[8] an sake jaddada ta a kwanan nan a shekara ta 2011[9]
  • Sarrafa cutar tsutsan ciki mai yaduwa ta hanyar bayar da magungunan tsutsan cikin ga yara 'yan makaranta da ke cikin hatsarin kamuwa da ita, wanda aka amince da ita a shekara ta 2001
  • Tsarin WHO akan matakan lafiyar ma'aikata, wanda aka amince da ita a shekara ta 2007
  • Kula da shan miyagun kayan maye, wanda aka amince da ita a shekara ta 2010
  • Inganta matakai a fadin duniya don kula da kariya daga cututtuka da iya dauka daga wani (non-communicable disease), wanda aka amince da ita a shekara ta 2011[9]

Har ila yau, Majalisar Lafiya ta Duniya ke da alhakin amincewa da Rabe-raben Iyali ta WHO ta Kasa da Kasa, wasu jerin ka'idaddun rabe-reben kiwon lafiya ta kasa da kasa (ICD), da kuma Rabe-raben Ayyuka, Nakasassu da kuma Lafiya ta Duniya - International Classification of Functioning, Disability and Health (IDF).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "World Health Assembly". Geneva: World Health Organization. Retrieved 21 June 2011.
  2. WHO. Working for health: an introduction to the World Health Organization. Geneva.
  3. "Countries". World Health Organization. Archived from the original on August 21, 2004. Retrieved October 27, 2011.
  4. Daalen, Kim Robin van; Chowdhury, Maisoon; Dada, Sara; Khorsand, Parnian; El-Gamal, Salma; Kaidarova, Galiya; Jung, Laura; Othman, Razan; O'Leary, Charlotte Anne; Ashworth, Henry Charles; Socha, Anna; Olaniyan, Dolapo; Azeezat, Fajembola Temilade; Abouhala, Siwaar; Abdulkareem, Toyyib (2022-08-01). "Does global health governance walk the talk? Gender representation in World Health Assemblies, 1948–2021". BMJ Global Health (in Turanci). 7 (8): e009312. doi:10.1136/bmjgh-2022-009312. ISSN 2059-7908. PMC 9403126 Check |pmc= value (help). PMID 35998979 Check |pmid= value (help).
  5. 5.0 5.1 "RULES OF PROCEDURE OF THE WORLD HEALTH ASSEMBLY". Basic Documents (PDF) (47 ed.). World Health Organization.
  6. "1 - Constitution of the World Health Organization". Basic Documents (PDF) (49 ed.). World Health Organization. 2020.
  7. "Milestones in the eradication of smallpox". World Health Organization. Archived from the original on July 31, 2009. Retrieved 21 June 2011.
  8. WHO. Poliomyelitis. Retrieved 21 June 2011.
  9. 9.0 9.1 "Sixty-fourth World Health Assembly closes after passing multiple resolutions". Geneva: World Health Organization. 24 May 2011. Archived from the original on May 25, 2011. Retrieved 21 June 2011.