Malam Lawal Kalarawi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Malam Lawal Ƙalarawi shahararren malamin addinin Musulunci ne a Jihar Kano wanda yayi Shura a ƙarshen ƙarni na ashirin. Malamin yana bin salon barkwanci a lokutan gudanar da wa'azin sa, inda yake yin maganganu na bayar da dariya harma da na katobara. Malamin ya sha ɗauri a hukumomin gwamnatin soji a sakamakon ɓamɓarmar sa da barkwancin sa. Wasu daga chikin falsafofinsa, "Idan mutum yayi karatun daya wuce hankalin mutane ba zasu iya dinga fahimtarsa ba. Shahararren malami ne.

"Alkur'ani bai boye komai ba,malamai ne idan sunzo karatu basa bayyanawa yadda ya kamata,

"Mulki idan ya hadu da son Allah da tsoron Allah sai Kasa ta gyaru, in kuma ya hadu da kin Allah da Annabi sai Kasa ta bachi, ai ta chuta a chikinta.

Ko baka da asiri ka saki ranka kada ka nufi kowa da mugun nufi wallahi duk Wanda yayi maka Sammu sai ya koma kansa. Abba Rabiu matallawa [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://freedomradionig.com/shekaru-20-da-rasuwar-malam-lawal-kalarawi-ko-yaya-mutanan-kano-ke-tunawa-da-shi/