Jump to content

Malam Wakili

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Malam Wakili
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2015 - 17 ga Maris, 2018
Ibrahim Musa - Lawal Yahaya Gumau
District: Bauchi South
Rayuwa
Haihuwa Bauchi, 1958
Mutuwa 2018
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Jihar Bauchi

Malam Ali Wakili (Haihuwa da Rasuwa: 1958 - 2018) dan siyasan Nijeriya ne kuma tsohon dan majalisar dattawa ne na tarayyar Najeriya daga jihar Bauchi. Ya wakilci Kudancin Bauchi a Majalisar Wakilai ta 8 kafin rasuwarsa a shekarar 2018. Sanata Wakali shi ne Shugaban Kwamitin rage talauci da rage rayuwar Al'umma da mataimakin shugaban Kwamitin Sojojin Sama na majalisar Dinkin Duniya na majalisar.[1]

Wakili ya halarci makarantar firamare ta Lere da ke karamar Hukumar Tafawa a cikin jihar Bauchi daga 1965 zuwa 1972, ya ci gaba zuwa Sakandaren Gwamnati, Makarantar Damaturu a wancan lokacin daga Borno, daga 1972 zuwa 1977, inda ya sami Digirinsa na Sakandare. Daga shekarar 1977 zuwa 1979, ya halarci Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Bauchi sannan daga baya ya tafi Jami’ar Bayero, Kano don karatun Digiri, inda ya kammala a shekarar 1982.[2]

An gudanar da zaben fidda gwani bayan mutuwarsa kuma Lawal Yahaya Gumau na jam’iyyar All Progressive Congress ya yi nasara. Yankin Sanatan Bauchi ta kudu ya kumshi kananan hukumomi bakwai na jihar.

Wakili tsohon ma'aikacin kwastam ne kuma ya kayar da tsohon gwamnan jihar, Malam Isa Yuguda yayin zaben 2015, don zama sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu.

Wakili ya rasu a ranar 17 ga Maris na shekarar 2018 [2]

  1. Azare, Musa (2018-03-24). "Senator Ali Wakili: 1960-2018 – Daily Trust". Dailytrust.com.ng. Retrieved 2020-01-08.[permanent dead link]
  2. 2.0 2.1 2:16 pm (2018-03-17). "Bauchi Senator, Wakili, passes away - Vanguard News". Vanguardngr.com. Retrieved 2020-01-08.