Maria da Conceição Nobre Cabral

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maria da Conceição Nobre Cabral a cikin 2008

Maria da Conceição Nobre Cabral 'yar siyasa ce ta Guinea-Bissauan wacce ta kasance ministar harkokin waje daga shekarun 2007 zuwa 2009.

An naɗa Cabral a matsayin Ministar Harkokin Waje a ranar 18 ga watan Afrilu, 2007, a matsayin wani ɓangare na gwamnatin Firayim Minista Martinho Ndafa Kabi. Shugaba Nino Vieira ne ya zaɓe ta a matsayin. [1]

Cabral ta auri tsohon jakadan Guinea-Bissau a Amurka. [1] A halin yanzu, ita ce Shugabar wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Scorpius-Centaurus. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Alberto Dabo, "Guinea-Bissau's new government named", Reuters (IOL), April 18, 2007.
  2. 6th Brazil Africa forum. "Conceição Nobre Cabral: liderança no combate à pobreza, promoção da saúde e direitos das mulheres" (in Portuguese). Retrieved 2020-01-01.CS1 maint: unrecognized language (link)