Jump to content

Marie Lebihan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marie Lebihan
Member of the National Assembly of Niger (en) Fassara

1989 - 1991
Rayuwa
ƙasa Nijar
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Movement for the Development of Society (en) Fassara

Marie Lebihan yar siyasan Nijar ce. Tana daga cikin rukunin mata na farko da aka zaɓa a Majalisar Dokoki ta ƙasa a shekarar 1989.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Memba na National Movement for the Development of Society (MNSD), Lebihan an tsayar da shi a matsayin dan takarar Majalisar Tarayya a Maradi a zaɓen shekarata 1989 . Kasancewar MNSD ita ce jam’iyya ɗaya tilo ta doka, an zabe ta ba tare da hamayya ba, ta zama daya daga cikin rukunin farko na mata biyar da aka zaɓa a Majalisar Dokoki ta Kasa. [1] An rusa majalisar ƙasa a shekarata 1991 kuma ba a sake zabenta a zaɓen shekarar 1993 ba .

  1. Alice J. Kang (2015) Bargaining for Women's Rights: Activism in an Aspiring Muslim Democracy, pp117–118